Mika filayen jiragen Nigeria 'ba dabara ba ce'

Asalin hoton, Getty Images
Kwararu da masu ruwa da tsaki na ci gaba da nuna damuwa kan aniyyar gwamnatin Najeria, na mika filayen jiragen saman Abuja da na Lagos ga yan kasuwa.
Lamarin dai ya janyo suka daga ma'aikatan hukumar kula da gudanarwar filayen jiragen kasa watau FAAN.
Injiniya Muhammad Sani Baba, tsohon shugaban hukumar ta FAAN ne kuma ya bayyana irin illar da mika filayen biyu ga 'yan kasuwa zai yi ga gwamnati da kuma ma'aikata:
"Wadannan filayen jirgin sama guda biyu da ake magana a kansu, sune jigo dake rike sauran kananan filayen jirgin saman guda 18", inji Injiniya Muhammad.
Ya kara da cewa "Kaga idan ka dauke jigogin guda biyu ka ba wa 'yan kasuwa, kabar gwamnati da sauran guda 18, wadanda basa kawo kudi wadanda kuma ana ciyar da su ne domin a gudanar da tsarin baki daya".
Ya kuma bayyana cewa a karkashi wannan tsarin, kananan filayen ne ke tura jirage daya ko biyu a kowane yini zuwa Legas, wanda shi ke sa filin na Legas ya sami kimanin jirage masu sauka guda 40 a kowane yini.
Ya ce idan aka dauki manyan filayen na Legas da Abuja aka mika su ga 'yan kasuwa, za a daina raba kudaden da ake samu daga ayyukan da suke yi tare da kananan filayen. Wannan zai iya kawo koma bayan da ka iya gurgunta ayyukan sufurin jiragen sama gaba daya.
Da aka sanar da shi cewa kasashen da suka cigaba na gudanar da irin wannan tsarin ne na mika filayen jirgin samansu ga 'yan kasuwa, sai ya ce sam ba haka batun yake ba:
"Ba haka bane. Bari in baka labarin kasar Ostireliya, nan wurinmu suka zo suka koyi tsarin. Indiya ma nan wurinmu suka zo suka koyi tsarin. Indiya suna da filayen jirgin sama 100, kuma a wurinmu suka koyi tarin gudanar dasu," in ji shi.




























