Rashin alkalai ya hana yanke hukunci kan zaben Kenya

Asalin hoton, EPA
Babban jojin Kenya ya ce kotun kolin kasar ba ta iya saurarar karar dake neman a soke zaben shugaban kasar da aka shirya yi ranar Alhamis ba.
David Maraga ya ce ba a samu isassun alkalai daga cikin alkalai bakwai na kotun da za su iya saurarar karar ba.
'Yan bindiga sun harbi dogarin mataimakiyar babban jojin kasar ranar Talata.
Mista Maraga ya ce Philomena Mwilu "bata iya ta samu halartar zaman kotun ba".
Dogarinta yana jinya a wani aisbiti a babban birnin kasar, Nairobi.
Wakilin BBC's Alastair Leithead a Nairobi ya ce a yanzu ana sa ran a gudanar da zaben kamar yadda aka tsara.
Kotun kolin ta soke zaben farko da aka gudanar a watan Agusta, tana mai cewa an samu "kurare da sabawa doka".
Jagoran 'yan adawa Raila Odinga yana kauracewa zagaye na biyu na zaben, inda ya ce babu wani abu da ya sauya.
Ana sa bangaren Shugaba Uhuru Kenyatta, wanda ke neman wa'adi na biyu, ya ce dole ne a gudanar da zaben.



























