Yadda mata ke shan tasku a sansanin 'yan gudun hijira a Abuja

Bayanan sautiYadda mata ke shan tasku a sansanin 'yan gudun hijira a Abuja
An wallafa

Kuna iya latsa alamar lasifikar nan ta sama don sauraron cikakkiyar tattaunawar da Halima Umar Saleh ta yi da matan a shirin Adikon Zamani.

A duk lokacin da aka ambaci lamarin mata, to babban abin da ke fara zuwa ran yawancin mutane shi ne matsalar da suke fuskanta ta bangarori daban-daban na rayuwa.

Tun bayan da rikicin Boko Haram ya yi kamari mutane da dama suka tsere daga garuruwansu don neman mafaka a inda suke tunanin ya fi musu kwanciyar hankali.

Sai dai duk yawancin 'yan gudun hijirar kan fake ne a sansanoni da ko dai gwamnati ce ta gina ko kuma kungiyoyi masu zaman kansu, a matsayin sabon muhalli.

A irin wannan yanayi na zaman gudun hijira dai mata ne suka fi shan wahalar rayuwa a sansanonin saboda irin lalurorin da aka fi sanin mata na fama da su ko da kuwa zaman jin dadi suke yi a gidajensu.

Lalurorin sun hada da na goyon ciki da haihuwa da raino da tsaro da ma batun jinin al'ada.

An kiyasta cewa mata ne suka fi yawa a sansanonin 'yan gudun hijira da ke yankuna daban-daban na Najeriya da ma makwabtan kasashe irin su Nijar da Kamaru.

Da yawansu kuma mazajensu sun mutu sun bar su da yara, yayin da wadanda nasu mazajen ma ke raye ba su tsira daga wahalhalun rayuwa ba a sansanonin.

A shirin Adikon Zamani na wannan makon BBC Hausa ta kai ziyara wani sansanin 'yan gudun hijira da ke babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, inda Halima Umar Saleh ta tattauna da wasu mata kan irin matsalolin da suke fuskanta kamar na goyon ciki da haihuwa da ma batun jinin al'ada.

Sun kuma shaida mata cewa, suna cikin tasku ba kadan ba, dangane da samun kayayyakin kawar da lalurorinsu wadanda mata ke yawan fama da su.

Matan aure da 'yan mata da ke rayuwa a wannan sansani dai duk suna zaman tsammanin warabbuka ne, na jiran kayayyakin taimako da kungiyoyi masu zaman kansu da kuma bayin Allah da ke kai musu don tare matsalolin nasu.

Baya ga wannan batu kuma, akwai batun rashin ingantaccen tsarin bandaki don zagayawarsu, inda a dole suke tafiya jeji su kawar da lalurarsu.

Sai dai wata budurwa ta shaida min cewa, duk da dai bandakin ba shi da tsafta kuma ana iya daukar wasu cututtuka ma, to ta gwammace ta shige shi hakan nan maimakon ta je jeji.

"Wata rana na je jeji na tsugunna kenan sai ga maciji, shi yasa na daina zuwa gara dai na je bandakin duk da cewa a can na kwaso wata cuta ta kaikayin al'aura da kuraje, saboda rashin tsaftarsa," a cewar Patience.

To ko ma dai mene ne yawan matsalolin da matan ke fuskanta, sun gwammace zama a wannan waje a takure maimakon su koma garuruwansu da suka baro sakamakon rikicin Boko Haram.