An gano diamond da nauyinsa ya kai karat 400 a Saliyo

Kawo yanzu dai masana basu fayyace darajar diamond din da aka gano ba
Bayanan hoto, Kawo yanzu dai masana basu fayyace darajar diamond din da aka gano ba
An wallafa

Masu hakar ma'adinai a Saliyo sun hako wani diamond wanda nauyinsa ya kai karat 476, kuma an ce shi ne diamond na 29 ma fi ya girma da aka gano.

Kawo yanzu dai kwararu basu tabbatar da darajar ko kuma kudin diamond din ba.

Lamarin dai na zuwa ne bayan da aka gano wani daimaond da nauyinsa ya fi karat 700, wanda shi ne diamon mafi girma da aka gano a Saliyo a cikin rabin karni.

A watan gobe dai zaa ayi gwajonsa a birnin Newyork na Amurka.

Shugaban hukumar ma'adinai ta kasar Saliyo, Sahar Wonday ya ce diamond din da aka gano ya nuna cewa akwai albarkatun kasa masu daraja a yankin Kono, inda a nan ne aka gano dukannin daimond din su biyu.

Kasar na son tayi amfani da cinikin watan Disemba domin ta yi kokarin kawar da abubuwan da suka faru a baya watau yakin basasa da aka shafe shekara 11 ana yi wanda kasuwanci diamond na cikin abubuwan da suka rika ruruta rikicin.