Nigeria ce ta uku da aka fi mutuwa saboda ta'addanci a duniya - Rahoto
An wallafa
Wani rahoto game da alkaluman kashe-kashen ta'addanci a duniya na 2017, ya bayyana Najeriya a matsayi na uku a duniya da 'yan kasashensu suka fi mutuwa saboda ayyukan 'yan ta'adda.
Duk da haka rahoton ya ce an sami gagarumar raguwar kashe-kashen mutane da kashi 80 cikin 100, sakamakon galabar da kasar ta samu kan kungiyar Boko Haram.
Dangane da rahoton, Mukhtar Adamu Bawa na BBC Hausa ya tuntubi Malam Kabiru Adamu, masanin harkar tsaro a Najeriya, inda ya fara da tambayarsa ko yaya ya ga wannan rahoto?

Asalin hoton, Getty Images