Mutum 15 sun mutu a turmutsutsu a kasuwar Morocco

Moroko
Bayanan hoto, Mutanen sun rasu ne a wata kasuwa
An wallafa

A kalla mutum 15 sun rasa rayukansu a wani turmutsutsu da aka yi a wata kasuwa a Morocco a lokacin da suka je karbar taimakon abinci.

Lamarin dai ya faru ne a birnin Boulaalam da ke kusa da ke kusa da gabar ruwan Essaouira.

Hotunan wajen da aka dauka sun nuna gawawwakin mata da yawa a wajen.

Har yanzu dai ba a san abin da ya janyo turmutsutsun ba, amma ganau sun ce an samu karuwar mutanen da ke zuwa karbar taimakon abincin ne da ake yi a duk shekara da wata kungiyar agaji ke kai wa.

Moroko dai na fama da karancin amfanin gona saboda fari, lamarin da ya janyo tsadar kayan abinci a kasar.

Ma'aikatar cikin gida ta kasar ta ce sarki Muhammed na 6, ya bai wa hukumomin karamar hukumar umurnin taimaka wa wadanda lamarin ya rutsu da su.

Ya kuma ce zai dauki nauyin biya musu kudin asibiti.

Babu cikakken bayyani game da abin da ya hadassa turmutsutsin.

Mutane sun rasu ne a wata kasuwa