Kalli bidiyon tauraruwar Gasar Hikayata ta BBC ta bana
An wallafa
Maimuna Idris Sani Beli ita ce ta lashe gasar Hikayata ta mata zalla ta BBC Hausa ta bana.
A bara ne dai Sashen Hausa na BBC ya kirkiro gasar ta Hikayata da nufin bai wa mata damar bayyana abin da ya fi damunsu a rayuwa.