Jirgin yakin sojin Amurka ya yi hatsari a tekun Japan

Asalin hoton, EPA
Ma'aikatar Tsaro ta Amurka ta ce, mutum takwas aka ceto bayan da jirgn ruwan sojin kasarta ya yi hatsari a gabar tekun Japan wanda yake dauke da ma'aikata da fasinjoji 11.
Ma'aikatar ta ce a rahoton da rundunar sojin Amurkan ta fitar ya nuna cewa matsalar injin da jirgin ruwan ya samu ne ya haddasa hatsarin.
Sojin ruwan ba su bayyaana kirar jirgin da ya yi hatsarin ba, amma rundunar ceto rayuka ta Japan ta ce jigin kirar C-2 ne.
Jirgin na kan hanyarsa ne ta zuwa tekun Philippine inda jiragen ruwa mai daukar jiragen yaki yake.

Asalin hoton, Getty Images
A watan Agusta ma ma'aikata 10 ne suka mutu, a lokacin da jirgin ruwan yaki na Amurka USS John McCain ya yi taho mu gama da wata tanka a kusa da Singapore..
A watan Yuni ma jirgin USS Fitzgerald ya yi karo da jirgin ruwan daukar kaya a gabar tekun Japan, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum bakwai.
A wani hatsarin da aka yi ma wanda ba a mutu ba, a watan Janairu jirgin ruwa na USS Antietam ya shige karkashin kasa kusa da tasharsu a Japan, a watan Mayu ma jirgin USS Lake Champlain ya yi taho mu gama da jirgin ruwan kamun kifi na Koriya ta Kudu.
Ministan tsaro na Japan Itsunori Onodera ya ce ya samu rahoto daga Amurka da yake nuna cewa matsalar da injin jirgin ke da ita na iya haddasa hatsarin.

A cewar shafin intanet na kungiyar jiragen, sama da jirage 60 masu samfuri dabam-dabam ne, da jirage masu saukar ungulu da ake sauka a kansu, wanda suka hada da na yaki da jiragen kai hari, da jiragen tafiye-tafiye da kuma jirage masu saukar ungulu da ake amfani da su ta fannoni dabam-dabam.
Jirgin Ronald Reagan na daya daga cikin jirage uku na Amurka da jiragen yaki ke sauka a kansa, yana kuma aiki ne a yankin kusa da jiragen Japan da na Koriya ta Kudu, a yayin da ake kara samun tashin hankali tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa.































