An kama bakon da ya sace talbijin 120 a otal a India

Asalin hoton, Bangalore police
An kama wani mutum da ake zarginsa da shafe wata hudu yana satar talbijin har guda 120 daga otal daban-daban a kudancin Indiya.
Wani babban jami'in 'yan sanda ya shaida wa wakilin BBC Hindi Imran Qureshi cewa, ma'aikatan otal din ba su taba zargin Vasudev Nanaiah ba, kasancewarsa bakon da ke cike da nutsuwa da kamala.
'Yan sanda sun ce a duk lokacin da Mr Nanaiah zai kwana a wani otal ya kan je ne da wani babban akwati da ake tsammanin kayansa ne a ciki.
A watan Oktoba ne aka kama shi yana satar talbijin a wani otal, amma an bayar da belinsa kafin daga bisani a sake kama shi kuma.
'Yan sanda sun ce ya sake komawa ruwa wajen yin satar kwanaki kadan bayan da ya fito daga gidan yari.
Mataimakin kwamishinan 'yan sanda Chetan Singh Rathor ya ce, idan Mr Nanaiah ya fahimci cewa akwatin da ya je da shi ya yi karami, sai ya auna girman talbijin din da ke dakin ya koma ya nemo wani akwatin da ya fi wannan girma.
Mista Rathor ya ce: "Ya kan shiga otal din ya fita a lokuta da dama ta yadda ma'aikatan otal din ba za su fahimci cewa ya fita da talbijin ba."
An kama Mr Nanaiah ne bayan da mutumin da ya yi niyyar sayar wa da talbijin din ya tona masa asiri a wajen 'yan sanda.
'Yan sandan Bangalore sun same shi da laifuka 21 na sata, kuma suna fatan zai yi zaman gidan yari na tsawon lokaci.
Wata kotu za ta yanke hukuncin ko yana bukatar a binciki lafiyar kwakwalwarsa.



























