'Yan Nigeria sun yi zanga-zanga kan 'sayar da bayi' a Libya

Bayanan sautiSaurari yadda 'yan Nigeria suka yi zanga-zanga kan 'cinikin bayi' a Libya
An wallafa

Wasu 'yan Najeriya sun gudanar da zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin Libya da ke birnin Abuja domin nuna bacin ransu game da tozartawar da ake yi wa bakaken fata ciki har da 'yan Najeriya a kasar Libya.

'Yan Najeriyar da suka hallara a gaban ofishin jakadancin kasar dai sun ce abin takaici ne a ce ana cinikin 'yan Najeriya kan dala 400, kudin da bai kai naira 150,000 ba.

Sun nemi gwamnatin Libya da ta Najeriya su kawo karshen cin zarafin 'yan Najeriya a kasar Libya.

Daya daga cikin masu zanga-zangar, Deji Adeyanju, ya ce ba a san Najeriya da wulakanta baki ba, saboda haka bai kyautu a ce ana musguna wa 'yan Najeriya a wata kasar Afirka kamar Libya ba.

Ya ce: "Abun mamaki ne a ce kudi kalilan ne ake sayan dan-Adam. Dan Adam guda wai azo a ce za a saye shi dala 400. Dala 400 nawa ne a kudin Najeriya?"

Libya
Bayanan hoto, Masu zanga-zangar sun nemi a kwaso 'yan Najeriyar da suka makale a Libya

Deji ya ce nuna rashin amincewa da yadda gwamnatin Najeriya take tinkarar lamarin inda ya ce idan aka yi wa dan Amurka irin wannan cinzarafin, Amurka za ta yaki kasar ne.

Masu zanga-zangar dai sun ce jami'an ofishin jakadancin kasar sun yi watsi da su.

Sai dai kuma BBC ta nemi jin ta bakin sakatariyar ofishin jakadancin kasar, Rose Diovu, kan zargin cewa ofishin jakadancin ya yi watsi da masu zanga-zangar, sai ta ce jami'an ofishin suna hutun maulidi ne shi ya sa babu masu tarbar masu zanga-zangar a ofishin.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari dai ya bayar da umarnin cewa a kwaso 'yan Najeriyar da suka makale a kasar Libya bayan wasu 'yan Najeriya 242 suka dawo daga kasar a wannan makon.

Burin masu fafatika dai shi ne a dawo da dukkan 'yan kasar da suka rage a can tare da samar musu ayyukan yi.