Dage zaben Najeriya zai kawo cikas ga amincewa da kasafin 2019 — Majalisa

Asalin hoton, Getty Images
Majalisar dokokin Najeriya ta ce dage zabe ya shafi ayyukanta musamman wasu muhimman bukatu da ke gabanta.
Mai magana da yawun majalisar wakilai Hon. Abdurrazaq Namdaz ya shaida wa BBC cewa dage zaben zai yi matukar illa ga ayyukan majalisa musamman batun amincewa da kasafin kudi da kuma wasu muhimman bukatu da ke gabansu.
"Dage zaben ya mayar da hannun agogo baya, musamman kasafin kudin Najeriya na 2019 da ke jiran amincewar majalisa," in ji shi.
Hukumar zaben Najeriya INEC ta nemi afuwar 'yan kasar bayan dage zaben da aka shirya gudanarwa na shugaban kasa da 'yan majalisar tarayya a ranar Asabar.
Hukumar ta ce ta dage zaben ne saboda matsaloli na kai kayan zabe da wuri a wasu jihohi takwas daga cikin 36 na Najeriya.
Mista Namdaz ya ce yanzu ba su da tabbas ko za su koma zama a ranar Talata kamar yadda suka shirya saboda dage zaben da ya shafe su matsayinsu na 'yan majalisa kuma 'yan takara.
"Idan ba mu koma ba dole a samu jinkiri, idan ba mu yi ba mutane za su ce mun rike kasafin kudi," in ji shi.
Ya ce 'yan majalisa ba su ji dadin dage zaben ba saboda sun yi kokari wajen amincewa da dukkanin bukatun hukumar zaben kasar domin gudanar da ayyukanta cikin lokaci.



























