Sojoji sun hallaka 'yan Boko Haram

Asalin hoton, Getty Images
Sojojin Najeriya sun yi nasarar hallaka mayakan Boko Haram da dama, a wani kwantan bauna da dakarun suka yi musu a jihar Yobe da ke Arewa maso gabashin kasar a yammacin ranar Talata.
A wata sanarwa da rundunar sojin kasar ta fitar ta ce rundunarsu ta yi wannan nasara ne sakamakon bayanan da suka samu a kan yunkurin mayakan Boko Haram din na kai hari Damaturu, babban birnin jihar ta Yobe.
Sanarwar ta kara da cewa, dakarun Najeriya masu yaki da Boko Haram sun samu nasarar yi wa mayakan Boko Haram din kwanton bauna ne inda suka hallaka da dama daga cikinsu.
Dakarun sun yi kwanton bauna ne a wani wuri da ba shi da nisa daga garin Mai Sandari wanda ke wajen babban birnin jihar ta Yobe wato Damaturu.
Sanarwar ta ce, dakarun sun ci karfin masu tayar da kayar bayan ne, saboda irin makaman da suke da su da kuma taimakon jiragen yakinsu.
Baya ga wadanda aka kashe, akwai wasu 'yan Boko Haram din da suka samu raunuka a artabun.
Dakarun sun kuma ce sun yi nasarar kwace makamai masu yawa daga 'yan Boko Haram din.
Yanzu dai sojojin sun dukufa wajen farautar 'yan Boko Haram din da suka tsere.



























