Kwace Filaye: An yi zanga-zangar a Abuja

Jama'ar garin Tungar Maje na yankin babban birnin tarayya Abuja sun gudanar da wata zanga-zanga karo na biyu a cikin makonni uku, inda suka dakatar da zirga-zirgar ababen hawa a kan hanyar Abuja zuwa Lakwaja.
Har ila yau sun tarbe babbar hanyar na tsawon sa'o'i da dama.
Jama'ar garin sun dauki wannan mataki ne don nuna rashin amincewarsu da abin da suka kira kokarin da sojoji ke yi na kwace masu filaye karfi da yaji, da kuma zargin sojojin sun harbe wani matashi daya tare da raunata wasu mutane akalla biyar a jiya.
Ya zuwa yammacin ranar Laraba dai kura ta lafa, kuma zirga-zirgar ababen hawa ta ci gaba da gudana kamar yadda aka saba a kan babbar hanyar Abuja zuwa Lakwaja, bayan da jama'ar garin Tungar Maje suka gudanar da wata zanga-zanga, wadda ta kai su ga rufe hanyar na tsawon kimanin sa'o'i biyar.

Matasan garin, maza da mata, sun rirrike da kwalayen da aka yi rubuce-rubucen da nuna rashin amincewa da abin da jama'ar garin suka kira, ''yi masu karfa-karfa ko uwar hannu'' a filayensu na gadon kaka da kakanni, wasu kuma suna kuwwar ba su yarda ba.
Karo na biyar ke nan dai mutanen garin na Tungar Maje suna daukar irin wannan mataki.
A karshe dai hukumomin babban birnin tarayya da sauran masu ruwa da tsaki ne suka shawo kan zanga-zangar.
Mun kiran layukan wayar mai magana da yawun rundunar sojan Najeriya, Kanar Sagir Musa, don jin nasu bayanin kan dakasaramar filayen na garin Tungar Maje da ke yankin babban birnin tarayya Abuja.
Sai dai layukan wayar tasa suna rufe, har ya zuwa lokacin aiko da wannan rahoton.



























