Brunei ta ce Shari'ar Musulunci kariya ce ga al'umma

Asalin hoton, European Photopress Agency
Gwamnatin Brunei ta ce kaddamar da shari'a musulunci, tafarki ne na kariya maimakon hukunci mai tsanani da wasu suka dauka.
Ma'aikatar harakokin wajen kasar ce ta mayar da martani bayan fuskantar suka da adawa daga kasashen yammaci kan tsarin shari'a da gwamnatin ta kaddamar a makon da ya gabata.
Karkashin dokar, za a zartar da hukuncin kisa ta hanyar jifa ga duk wanda aka kama da laifin zina da luwadi.
Amma Brunei ta ce hukuncin zai yi wahala domin sai da kwararan shedu.
Wannan na zuwa bayan Majalisar Dinkin Duniya ta yi kakkausar suka da matakin, wanda ta kira zalunci da keta hakkin dan adam.
Martanin Brunei
Brunei ta mayar da maratani kan kalaman Majaliar Dinkin Duniya inda minisan harakokin wajen kasar Erwan Yusof ya ce "shari'a tafarki ne na kariya maimakon hukunci.
Ya ce hanya ce ilmantarwa da gyara halaye da kulawa maimakon hukunci.
"Haramta zina da luwadi mataki ne na kariya ga iyali da musulmi ma'aurata musamman mata," in ji sanarwar.

Asalin hoton, Getty Images
Sanarwar ta kuma ce kafin zartar da hukuncin haddin sata wato yanke hannu, dole sai an samu shedu maza akalla guda biyu wadanda kowa ya shaida cewa mutanen kirki ne kafin zartar da hukuncin.



























