Me ya sa duniya ke kara shiga bacin rai da kunci?

Asalin hoton, Getty Images
Mutane a fadin duniya na kara zama cikin fushi da matsi da damuwa a cewar wani sabon nazari kan al'ummomin duniya.
Daga cikin mutum 150,000 da aka zanta da su a kasashe fiye da 140, kashi daya cikin uku sun ce suna fama da matsin rayuwa, yayin da akalla mutum daya cikin biyar ya ce yana fama da fushi ko bacin rai.
Rahoton Gallup Global Emotions na tambayar mutane ne game da abubuwan alheri da kuma na sharri da suka fuskanta.
Rahoton ya ce kasar da ta fi fama da kaka-ni-ka-yi ita ce Chadi, sai Nijar da ke biye mata. Kasa mafi rayuwar albarka kuma ita ce Paraguay.
Amurka ce ta 39 cikin kasashe mafi albarkar rayuwa, sai Burtaniya a matsayi na 46, Indiya tana matsayi na 93.
Masu bincike sun mayar da hankali ne kan fadi-tashin mutanen da aka tambaya suka yi kwana guda kafin nazarin.
An yi wa mutanen tambayoyi irinsu "shin ka/kin yi ta murmushi ko kyalkyala dariya jiya?" da "ko an mutunta ka/ki?" don samun haske cikin fadi-tashin yau da kullum na mutane.
Kimanin kashi 71 na mutanen sun ce sun yi matukar nishadi ana gobe binciken.
Nazarin ya gano cewa matsin rayuwa ya sake karuwa, yayin da damuwa da bacin rai suka yawaita. Kashi 39% na wadanda aka tuntuba sun ce sun shiga damuwa kwana guda kafin bincike, wasu 35% sun fuskanci matsi.
Manyan kasashe biyar da suka fi rayuwa cikin albarka
- Faragwai
- Fanama
- Guatemala
- Megziko
- El Salvador
Manyan kasashe biyar da suka fi rayuwa cikin kaka-ni-ka-yi
- Chadi
- Nijar
- Saliyo
- Iraki
- Iran
Kasashen Latin Amurka ciki har da Faragwai da Fanama da Guatemala ne ke kan gaba a jerin rayuwa cikin albarka, inda mutane ke ba da rahoton "jin dumbin shaukin alheri a kullum."
Chadi ce ta samu maki mafi yawa a jerin masu rayuwar kaka-ni-ka-ka-yi. Fiye da mutum bakwai cikin 10 na 'yan kasar suka ce sai sun sha fama kafin su iya samun abinci a wasu lokuta bara.
Kamar kashi 61% na 'yan Chadi ne suka ce suna jin ciwon jiki.
Duk da yawan makin kasar Chadi kan rayuwa cikin kaka-ni-ka-yi, mutane a Amurka da Girka sun fi 'yan Chadi fama da matsi.
Girkawa ne suka fi sauran al'ummomin kasashen duniya fama da matsi, inda kashi 59% suka ce sun ji matsin rayuwa ana gobe a gudanar da binciken. Kimanin kashi 55% na magidanta a Amurka sun ce sun sha fama da matsin rayuwa.




























