Gwamnoni na taron bitar sanin makamar aiki a Abuja

Asalin hoton, KANO DG MEDIA
Sabbi gwamnoni da kuma takwarorinsu da suka samu zarcewa a kan karagar mulki na gudanar da wata bitar sanin-makaman aiki a Najeriya.
Kungiyar gwamnonin kasar ce ta shirya bitar da nufin inganta harkar mulki a matakan jihohin kasar.
Jami`in yada labaran kungiyar gwamnonin, Abdurrazak Bello Barkindo, ya shaida wa BBC cewa bitar ta kunshi zama da sabbi da tsoffi gwamnoni wasu kasashe na katare don musayar ra'ayi kan tafiyar da mulki da sanin nauyin da ke kansu wajen ciyar da jihohinsu gaba.
Ya ce batutuwan da za a gabatar sun kunshi harkar tafiyar da mulki da irin ayyukan da matan gwamnoni ke yi kamar ba da agaji.
A cewarsa ana son a sake fahimtar da matan gwamnoni kan irin bukatun da mutane ke da shi, ganin cewa da yawansu na gudanar da ayyukan da suka shafi jama'a ko taimako.
Wannan ba shi ne karon farko da ake gudanar da irin wannan bitar ba, ko a shekara ta 2011 sai da aka shirya irin wannan bitar abin da ya sa wasu ke ganin cewa kamar kwalliya ba ta biyan kudin sabulu.
Sai dai a lokacin da yake mayar da martani kan hakan, Abdurrazak ya ce daga shekarar 2015 zuwa yanzu kusan ana iya cewa ana samu ci gaba da karuwa a bangaren ilimin rike mulkin jihohi.
''A shekarar 2011 ba a samu irin hadin-kan da ake gani a shekarun baya-bayanan ba, saboda akwai manyan mutane da lauyoyi da 'yan kasuwa da kuma masana harkokin gudanar da mulki da kowanne na ba da gagarumin gudunmawa a zaman bitar.''
''Yanzu suna samun hadin-kai ana zaman muhawara da sannin abin da ya kamata shi ya sa su kan suke son zaman taron domin a tsayar da akida daya.''
Tuni dai masana suka fara tofa albarkacin bakinsu a kan wannan bitar kan zargin da suke yi cewa wasu daga cikin gwamnonin ba jagorancin ba ne a gabansu.

Asalin hoton, KANO DG MEDIA
Dokta Abubakar Kari, masanin harkar siyasa ne a jami`ar Abuja, kuma a tattaunawarsa da BBC ya ce wasu gwamnonin kan manta da abin da aka koya musu da zarar sun haye karagar mulki.
Ya ce irin wannan taro ba wai gwamnoni kawai ake yi wa ba, a kan yi wa 'yan majalisar tarayya da na jihohi kan sanin makamar aiki.
Sai dai ya ce wani abin mamaki shi ne da zarar an gama bitar idan suka hau karagar mulki, sai su watsar da komai, suna aikata abubuwa da suka sha bamban da wadanda bitar ta gina su a kai ko suka koya.
Dokta Kari ya ce a mafiya yawan lokuta kusan ana iya cewa wannan taro ba shi da wani tasiri ko alfannusa ba shi da wani yawa domin suna jingine dukkan abubuwan da suka koya.

Asalin hoton, KANO DG MEDIA
Ya kuma kara da cewa "baya ga ajisanci da rashin kula, yawancinsu niyyar da ta sa suka yi wannan takarar akasi ne da abubuwan da ya kamata a ce sun yi."
''A mafiya yawan lokuta saboda son zuciya, sai ka samu abubuwan da suka koya a irin wannan taro na sanin makaman aiki ya yi daban da manufarsu ko niyyarsu.''
''A tsare-tsaren mulki akwai hanyoyi da dama da za a iya amfani da su idan wanda yake kan mulki ko wani gwamna ya saba ka'ida ko ya fandare a tankwaroshi.''
Dokta kari ya ce irin wannan taro da za a bi shi yadda aka tsara ko shimfida, babu shaka yana da tasiri.
Karanta karin wasu labarai:



























