Yadda Boko Haram ta kai hari daf da buda baki a Borno

Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni daga jihar Borno a Najeriya na cewa a kalla mutum 10 ne suka rasa rayukansu a wani harin da ake zargin wasu 'yan kungiyar Boko Haram sun kai a ranar Talata da maraice.
Maharan sun kuma kona gidaje da shaguna fiye da 100 a kauyukan da ba su da nisa da birnin Maiduguri.
Sai dai wasu rahotanni sun ambato rundunar sojin da ke yaki da kungiyar ta Boko Haram na cewa sun dakile harin tare da raunata wasu daga cikin maharan.
A baya dai birnin na Maiduguri ya sha fuskantar hare-hare daga kungiyar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane.
Bayanai sun nuna cewa maharan sun kai harin ne a daidai lokacin da ake shirin bude baki a kauyukan Molai da Maiboriti da ke karamar hukumar Jere a jihar Borno.
Haka kuma sun yi ta harbi da bindiga tare da cinna wuta a kan gidaje da shaguna da kasuwa.
Baya ga wadanda suka muutu, wasu da dama kuma sun jikkata a kauyukan biyu da ke da tazarar kilomita hudu daga Maiduguri.
Wadanda suka shaida lamarin sun ce 'yan bindigar wadanda ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kai harin ne a cikin motoci da kuma babura kuma sun yi ta cin karensu ba babbaka a yayin harin.
Sai dai wasu rahotanni sun ambato shugaban rundunar tsaro ta Lafiya Dole wadda ke yaki da Boko Haram a arewa maso gabashin kasar Birgediya Janar Bulama Biu na cewa dakaru sun samu nasarar dakile harin da masu tayar da kayar bayan suka yi yunkurin kai wa a kan al'ummar Molai da kewaye.
Haka kuma a cewarsa sojoji sun kashe wasu daga cikin maharan tare da bin sawun wadanda suka arce.
Ko da yake rundunar ta lafiya dole ta musanta rahotannin da ke cewa maharan sun yi yunkurin kai wa Maiduguri hari ne, amma a baya birnin wanda ya kasance tungar kungiyar na daga cikin wuraren da suka fuskanci hare-hare mafiya muni daga kungiyar ta Boko Haram a kasar.
Harin dai ya zo ne a yayin da shugabar babban zauren Majalisar Dinkin Duniya, Maria Fernada Espinosa ta fara ziyarar yini biyu a kasar, inda ta bayyana ayyukan kungiyar Boko haram na ta'azzara matsalolin da yankin Tafkin Chadi ke fuskanta.
Ta kuma nemi kasashen duniya su kara kaimi wajen kawo karshen mawuyacin halin da miliyoyin mazauna kewayen tafkin ke ciki.



























