An kori ma'aikacin BBC kan alakanta jikan sarauniya da biri

An kori mai gabatar da shirye-shirye a gidan rediyon BBC Danny Baker daga aiki bayan wani "barkwanci mai cike da shashanci" da ya yi game da jaririn gidan sarautar Ingila.
Tuni ya goge hoton, wanda ke dauke da wasu mata da miji rike da hannun juna tare da wani biri sanye da sutura irin ta mutane kuma, inda a ciki yake cewa: "an sallami jaririn gidan sarauta daga asibiti".
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
An zarge shi ne da yin kalaman wariyar launin fata ga gimbiyar ta Sussex.
Wani mai magana da yawun BBC ya ce: "Wannan kuskure ne, mai girman gaske".
Dan shekara 61 din yana gabatar da wani shiri ne na mako-mako.
Kafar yada labaran ta kara da cewa "wallafar ta saba wa dabi'un BBC wadanda aka san ta da su".
"Danny kwararren mai gabatar da shirye-shirye ne sai dai ba zai ci gaba da aiki da mu ba."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2

Bayan ya bayar da hakuri, inda ya kira abin da ya rubuta "barkwanci mai cike da shashanci", Baker ya kuma yin rubutu game da korar tasa: "Kiran da a kore ni....wannan darasi ne daga manyan kobo."
"Suna nufin cewa lallai abin da nake nufi kenan kuma wajibi ne BBC su kiyaye kaza-kaza," ya wallafa.
Da yake magana da gidajen yada labarai a wajen gidansa, ya ce: "Ban gane wadannan abubuwan ba da ke faruwa ba. Amma hukuncin BBC da ta yi min na rashin adalci, Allah ga ni gare ka."
Da aka tambaye shi kan wane mataki zai dauka, sai ya kara da cewa: "Abun haushi ne amma kuma ya birge ni saboda an zarge ni da abun da ban aikata ba. Don haka ba zan damu kaina ba. Abun da na yi bai kamata ba, shashanci ne amma kuma ba wariyar launin fata ba ne. Na san sarai me hoton ke nufi.
Harry da Meghan, wacce mahaifiyarta Doria Ragland bakar fata ce 'yar Amurka ta bayyana a ranar Laraba cewa, sunan sabon dansu Archie Harrison Mountbatten-Windsor.
Bayan da mutane suka yi masa caa kan abun da ya wallafa din ranar Laraba a shafukan sada zumunta, Baker ya ce: Ku yi hakuri na san abun da na yi ya harzuka wasu. Ban taba tunani haka ba amma dai ni babu komai a raina.



























