Koriya ta yi gwajin nukiliya sau biyu cikin kwana biyar

North Korean leader guides strike drill in the East Sea of Korea on 4 May.
Bayanan hoto, Shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jong-un na kallon yadda aka harba makaman a wannan makon
An wallafa

Sojojin Koriya ta kudu sun bayyana cewa Koriya Ta Arewa ta sake harba makami mai linzami mai cin gajeren zango a karo na biyu kasa da mako guda a wani yunkuri na dawo da gwajinta na nukiliya.

Makamin da aka harba daga arewa maso yammacin birnin Kusong ya yi tafiyar kilomita 420 da 270 inda ya doshi gabas.

Gwajin na zuwa ne sa'o'i bayan isar jami'an Amurka koriya ta Kudu domin farfado da tattaunawa kan shirin kasar na makamin nukiliya.

Masu sharhi na cewa Koriya ta arewa na son kara matsin lamba ne ga Amurka a kan gaza cimma yarjejeniya da ta yi.

Wata tattaunawa da aka yi tsakanin shugaban Koriya Ta Arewa da na Amurka a watan Fabrairu ta gaza cimma yarjejeniya, inda Amurka ta dage a kan lallai sai dai Koriyar ta watsar da shirinta na nukiliya, yayin da ita kuma Pyongyang ta dage a kan dole a cire mata takunkumi.

Abin da ya kamata mu sani kan sabon gwajin?

An harba makaman biyu da misalin karfe 16:30 agogon kasar kuma ya yi tafiyar kilomita 50 kafin ya fada a cikin teku, kamar yadda wata sanarwa sojin Koriya Ta Kudu ta shaida.

An harba makaman ne daga Kusong, mai nisan kilomita 160 daga birnin Pyongyang. An yi nazari mai zurfi kan wannan da hadin-guiwar jami'an tattara bayanan sirrin Amurka.

A ranar Asabar, Koriya ta arewa ta harba makamai da dama masu cin gajeran zango, wanda shi ne gwaji na farko tun kaddamar da wani shu'umin makami mai linzami a Nuwamban 2017

Gwajin bai so da mamaki ba la'akari da cewa kafafen yada labaran Koriya Ta Arewa sun sha nuna irin bacin ran kasar a kan atisayen hadin-guiwar da sojojin Amurka ke yi da Koriya ta kudu.

Pyongyang ta gargadi Washington cewa hakuri da take yi kan yarjejeniyar sassauta mata takunkumi ba mai dorewa ba ne.

Map of Kusong in North Korea

Fadar gwamnati Koriya Ta Kudu ta ce gwajin wannan makami abin damuwa da ke sake barazana ga kokarin shawo kan takaddamar da ake.

Sa'o'in da suka gabata, wakilin Amurka na musamman a Koriya Ta Arewa Stephen Biegun, ya isa birnin Koriya Ta Kudu, Seoul, domin tattauna hanyoyin cimma jituwar kwance damarar nukuliya da ke ci gaba da haifar da takaddama tsakanin kasashen duniya.

Ana dai sa rai ya tattauna hanyoyin samar da mafitar jin-kai ga Koriya Ta Arewa yayin da rahotanni ke nuna cewa kasar ta fuskanci matsalar fari irinsa mafi muni a shekaru, abin da ya kai jefa ta cikin karancin abinci.