Damfara ta intanet na karuwa a kudancin Najeriya- EFCC

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya wato EFCC ta koka kan yadda zamba cikin aminci da kuma damfara ke karuwa ta intanet musamman a kudu masu gabashin kasar.
Shugaban hukumar mai kula da yankin kudu maso gabashin kasar Usman Imam ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da rahoto kan ayyukan hukumar na zangon farko na wannan shekarar.
Usman ya bayyana cewa ''abin takaicin shi ne akasarin masu irin wannan damfarar za a ga cewa dalibai ne na jami'a ko masu yi wa kasa hidima ko kuma matasa ne da suka gama jami'a.''
Ya bayyana cewa a cikin shekarar nan kadai, sun samu nasarar kwato motoci masu tsada na alfarma daga wadanda ake zargi da damfarar.
Ya ce ''abin mamaki ne a ce dalibi na hawa motar da ta kai kusan naira miliyan 10.''
Ya ba iyaye shawara da su ci gaba da sa ido kan irin abubuwan da 'ya'yansu ke yi a intanet ganin yadda wannan lamarin na damfara ta intanet ke neman wuce makadi da rawa.
Ko da BBC ta tuntubi mai magana da yawun hukumar na reshen kudu maso gabashin kasar Chris Oluka kan yadda suka san cewa wannan yankin ne ya fi yawan masu damfara ta intanet, ya bayyana cewa bincike ne da suke yi bayan jama'a sun basu bayanan sirri.
Ya kuma ce irin wadaka da yaran suke yi da kudade da manyan motoci ke jawo hankalin EFCC har ta kama su.
Mista Oluka ya kuma ce ko a makon da ya gabata sun kama wasu matasa wadanda suke zargi da damfara ta intanet a garin Owerri.



























