Me ya sa 'yan wasan Najeriya mata suka fi mazan nuna bajinta?

Super Eagles
Bayanan hoto, Perpetua Nkwocha ta lashe kyautar gwarzuwar 'yar wasan Afirka har sau hudu
An wallafa
  • Wannan makala ce da wani mai sharhi kan harkokin wasanni a Najeriya Isiyaku Muhammad Ango ya rubuta mana.

A yanzu kusan ana iya cewa matan Najeriya sun fi maza kwazo domin kuwa akwai wadanda suke manyan kungiyoyi kamar Barcelona da kuma wadda ta lashe kyautar wadda ta fi zura kwallo a gasar Firimiya ta China a bara da dai sauransu.

Sannan kuma babban abin lura shi ne yadda ya kasance yawancinsu ba zaman benci suke yi ba a kungiyoyin da suke wasa, kamar yadda da yawa daga cikin 'yan wasa maza suke yi.

Misalan inda matan suka fi mazan kokari

1. Misali na farko a nan shi ne, tun a shekarar 2001 da aka fara bayar da kyautar gwarzuwar 'yar wasan Afirka bangaren mata, zuwa yanzu an yi sau 16, kasancewar ba a bayar da kyautar a shekarun 2009 da 2013 ba.

Daga cikin guda 16 da aka yi kuwa, 'yan wasan matan Najeriya ne suka lashe guda 10;

Tsohuwar 'yar wasar kasar Perpetua Nkwocha da ta lashe kyautar sau hudu a shekarun 2004, da 2005, da 2010 da kuma 2011, kuma har zuwa yanzu ita kadai ce ta taba lashe kyautar sau hudu.

Sai mai biye mata, Asisat Oshoala 'yar wasar kungiyar mata ta Barcelona da ta karba kyautar sau uku a shekarun 2014, da 2016 da kuma 2017.

Daga nan sai Cynthia Uwak wadda ta lashe sau biyu a shekarun 2006 da 2007.

A
Bayanan hoto, 'Yan Super Falcons sun kai zagaye na biyu a Gasar Cin Kofin Duniya wadda aka yi a Faransa a 2019

Akwai kuma tsohuwar fitacciyar 'yar wasa da ake ganin ita ta bude wa 'yan wasa matan Najeriya ido a harkar kwallon kafa a kasar, wato Mercy Akide wadda ta lashe kyautar sau daya a shekarar da aka kaddamar da gasar wato shekarar 2001.

2. Misali na biyu shi ne gasar cin Kofin Nahiyar Afirka ta mata wato Total Africa Women Cup of Nations ko kuma African Women's Championship da ake kiran gasar kafin shekarar 2015.

An fara gasar ce daga shekarar 1991.

Zuwa yanzu an buga gasar sau 13.

Daga cikin 13 da aka fafata, Najeriya ta lashe sau 11 a shekarun 1991 da 1995 da 1998 da 2000 da 2002 da 2004 da 2006 da 2010 da 2014 da 2016, da kuma na karshe da aka buga bara wato 2018.

Wannan ke nufin cewa sau biyu ne kawai Najeriya ba ta lashe ba a shekarun 2008 da 2012.

Amma duk da haka, Najeriya ce ta zo ta uku a shekarar 2008, ta kuma zama ta hudu a shekarar 2012.

A

3. A kakar bara, daga cikin manyan 'yan wasan Najeriya, wanda ya fi zura kwallo shi ne Odion Ighalo a kungiyar Changchun Yatai a gasar Firimiyar China wato Chinese Super League, inda ya zo na biyu a wadanda suka fi zura kwallaye da kwallo 21 a gasar.

Ita kuwa Asisat Oshoala ita ce ta lashe kyautar wadda ta fi iya zura kwallo wato Best Striker a gasar fimiyar mata ta China wato Chinese Women's Super League.

4. A cikin 'yan wasan Najeriya mata da maza a yanzu akwai wadanda suke cewa babu 'yar wasa kamar Asisat Oshoala a Nahiyar Turai.

Yanzu haka tana kungiyar Barcelona ta mata kuma tana cikin zaratan 'yan wasan kungiyar domin duk wasa tana ciki, kuma tana kan gaba wajen taimakon kungiyar.

A watan jiya, 'yar wasan ta taka rawar ganin lokacin da kungiyarta ta lallasa kungiyar mata ta Bayern Munich a wasan kusa da karshe na Zakarun Turai ta mata wato Uefa Women's Champions League.

Haka ne ya ba Barcelona damar tsallake wa zuwa wasan karshe.

Haka zalika 'yar wasan ta yi wasa a kungiyoyin Arsenal Ladies da kuma Liverpool.

Asisat Oshoala
Bayanan hoto, Asisat Oshoala

Manyan 'yan wasan Najeriya da ke taka leda a nahiyar Turai yanzu kuma suke cikin 'yan wasan da ke wakiltar Najeriya akwai Wilfred Ndidi wanda yake kungiyar Leicester City da ke Ingila.

Ndidi yana cikin zaratan 'yan wasan kungiyar, duk da cewa a yanzu kungiyar ba ta cikin manyan kungiyoyi a Ingila. Amma ba laifi kasancewar tana cikin firimiya.

Sai Alex Iwobi na Arsenal da Kenneth Omeruo da ke kungiyar Leganes a matsayin aro daga Chelsea.

Kungiyar Leganes tana rukunin farko na gasar La Liga ta Spain, amma karamar kungiya ce matuka.

Amma dai ana iya cewa yana kokari sosai domin yana cikin zaratan 'yan wasan kungiyar.

Sauran 'yan wasa kamar su Mikel Obi, wanda shi ne kyaftin din Super Eagles yanzu haka yana kungiyar Middlesbrough ce a rukuni na biyu na Firimiyar Ingila.

Mikel Obi,

Ahmed Musa kuma yana kungiyar Al-Nassr ta Saudiyya.

Akwai su da yawa da suke kwallo a kasashen waje, sai dai yawancinsu suna zaman kashe wando ne kawai a kungiyoyin da suke, yayin da wasu kuma suke dan samun 'yan mintuna kadan a wasa.

Su kuwa yawancin 'yan wasa matan kamar su Franciska Ordega wadda ake yi wa lakabi da Franny wadda kwanan nan ta bar kungiyar Atletico Madrid a kasar Spain ta koma China.

Golansu Tochukwu Oluehi da ke kungiyar Medkila IL da Rashidat Ajibade da ke kungiyar Abaldsnes ILa duk a kasar Norway da sauransu suna cikin zaratan 'yan wasan kungiyoyin da suke, domin kuwa ba kasafai suke zaman kashe wanda ba duk da cewa suma akwai masu zaman benci din.

Dalilin da ya sa wasu ke ganin mazan sun fi kokari

Babban dalilin da ya sa ake ganin kamar mazan sun fi kokari bai rasa nasaba da yanayi da al'adun mutanen Najeriya, inda har yanzu wasu da yawa daga mutane suke mamakin ganin mata suna taka leda.

A tunaninsu sana'ar maza ce kuma bai kamata mata su shiga ba.

Wannan ya sa a lokuta da dama ba a cika kallon wasan matan ba, ballantana ma a san kokarin da suke yi.

Wannan kuma ba a Najeriya kadai abin ya tsaya ba, domin a duniyar kwallon kafa da ma dukkan sauran wasanni, an fi kallon wasannin maza.

Misali Asisat Oshoala da ta taimaka wa Barcelona zuwa wasan karshe na Kofin Zakarun Turai na mata, da namiji ya samu wannan damar, da 'yan Najeriya sun fi yin magana.

Amma kasancewar ba kowa ba ne ma ya san akwai gasa kamar haka, sai ka ji shiru.

Akwai masu ganin tsofaffin 'yan wasan kasar irinsu Rashidi Yakini da Daniel Amukachi da Tijjani Babangida da dai sauransu sun fi hazaka, yawancin masu kallon kwallon yanzu sun taso ne da shauki da son wadancan 'yan wasan saboda sadaukarwa da suka yi wa kasar a lokutan baya.