Makon jiya: Wasikar Obasanjo ga Buhari,aiwatar da albashi mafi karanci

Asalin hoton, Presidency
'Yan Najeriya na ciki da wajen kasar sun shaida abubuwa da dama da suka faru ko dai a cikin kasar ko kuma a makwabta a makon da ya gabata.
Mun zabo batutuwa shida da suka fi shura daga cikin abubuwan da suka faru ga 'yan kasar na ciki da wajenta kamar haka:
1- Dole ne Buhari ya daina nuna halin ko-in-kula

A ranar Litinin 15 ga watan Yuli ne tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya rubuta wa Shugaba Muhammadu Buhari, wasika inda ya yi gargadin cewa "Najeriya na daf da fadawa wani wawakeken rami mai cike da hadari kuma shugaban kasar ne kawai zai iya dakatar da wannan mummunan bala'i".
Obasanjo ya ce matsalar tsaro a kasar na iya janyowa a kai wa Fulani harin ramuwar gayya, wanda ka iya jefa kasar cikin tashin hankalin kisan-kare-dangi irin wanda Rwanda ta fuskanta a baya.
Wasikar ta Obasanjo wadda ta janyo cece-kuce dai ta biyo bayan kisan Funke wadda 'ya ce ga Reuben Fasoranti, shugaban kungiyar Yarabawa ta Afenifere.
2- Kungiyar Dattawan Arewa ta nemi Fulani su bar kudancin kasar:

A ranar Laraba ne kungiyar dattawan arewa ta (NEF), ta nemi Fulani da su bar Kudancin kasar domin komawa Arewa, abi da ake ganin martani ne kan adawar da shugabannin al'ummar yankin suka nuna ga shirin gwamnatin tarayya na samar da Rugagen Fulani a yankunansu.
Tuni dai jihohin arewa da dama suka yi maraba da shirin.
Sai dai Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga Fulani makiyaya su yi watsi da kiran da kungiyar dattawan arewa ta yi musu na su baro Kudancin Najeriya domin komawa arewa.
A wata sanarwar da mai magana da yawun shugaban ya fitar, Buhari ya ce ''Dukkan 'yan Najeriya suna da damar watayawa a kasar da zama a duk sassanta ba tare da la'akari da ainahin inda suka fito ba".
3- Boko Haram ta kashe sojojin Najeriya biyar a Borno:

Rundunar sojin Najeriya ta ce mayakan Boko Haram sun kashe sojojinta biyar a kusa da garin Jakana mai nisan kilomita 30 daga birnin Maiduguri na jihar Borno a ranar Laraba.
A wata sanarwa da rundunar sojin kasar ta fitar a shafukanta na sada zumunta ta ce sojojin da suka mutu sun hada da Kanal da Kaftin da wasu sojojin uku a wani kwanton bauna da mayakan suka yi musu, a yayin da suke tafiya Damaturu daga Maiduguri.
Rundunar sojin ta ce tun da fari mayakan Boko Haram din ne suka yi kokarin kai hari sansanin sojoji na Bataliya ta 212 da ke Jakana ranar Larabar domin "satar kayan yaki da suke tsananin nema."
Mayakan sun je ne da misalin 6.45 na yamma a motocin igwa bakwai kuma an fafata da su sosai a yayin da suke son kutsawa sansanin da karfi.
4-Buhari ya amince da fara aiwatar da mafi karancin albashi

Asalin hoton, Presidency
A ranar Laraba 17 ga watan Yuli, Shugaba Muhammadu Buhari na najeriya ya amince da fara aiwatar da bayar da naira dubu 30 a matsayin mafi karancin albashi, ga ma'aikatan kasar na tarayyar da ke karbar kasa da hakan a yanzu.
Shugaban Hukumar Tsara Albashi ta kasar Cif Richard Egbule ya sanar da haka yayin ganawa da manema labarai a Abuja.
Ya ce ofishin babban akantan kasar zai duba ya ga lokacin fara aiwatarwar, wanda kuma za a fara biyan ne tun daga lokacin da Shugaban kasar ya sanya hannu a kan yarjejeniyar biyan.
5- Ruftowar gini ta kashe mutum 11 a Jos:

A yammacin ranar Litinin ne dai ginin wanda ya kunshi kantuna da kuma wuraren zaman jama'a ya rufta, abin da ya haifar da asarar dukiya da rayuka.
Kungiyar agaji ta Red Cross a Najeriya ta ce an zakulo karin gawawwakin mutane hudu a baraguzan wani ginin da ya rufta a Jos babban birnin jihar Filato, abin da ya sanya adadin wadanda suka mutu ya kai 11.
6 - Najeriya ta yi na uku a gasar AFCON:

Asalin hoton, Getty Images
Duk da cewa ba haka 'yan Najeriya suka so ba amma sun yi farin ciki da samun matsayin na uku domin ana yi da kai ya fi ba a yi da kai
Odion Ighalo ne ya zura kwallo daya tilon da ta bai wa Najeriya damar doke Tunisia a wasan neman na uku na gasar cin kofin kasashen Afirka.
Ighalo, wanda shi ne ya fi kowa cin kwallo a gasar bayan da ya zura biyar, ya ci kwallon ne bayan da golan Tunisia Moez Ben Cherifia ya kawar da kwallo daga hanyar dan wasansu na baya Yassine Meriah.
7 - Mikel Obi ya yi ritaya daga buga wa Super Eagles wasa:

Asalin hoton, Getty Images
Kyaftin din Super Eagles, Mike Obi ya ce ya jingine takalmansa daga buga wa Najeriya wasa kamar yadda ya tabbatar a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.
Ya ce "A matsayina na dan shekara 32 ya kamata na yi ritaya daga buga wa kasata wasa domin bai wa matasa dama, wadanda suka yi namijin kokarin lashe tagulla a AFCON 2019," Mikel ya bayyana a shafinsa na sada zumunta.
Dan wasan tsakiyar mai shekara 32 ya buga wa Najeriya wasa 89 tun daga shekarar 2005 zuwa 2019, inda ya zura kwallo shida kacal.



























