An wanke matar da aka ce ta yi kisa saboda ta yi bari

Salvadorean rape victim Evelyn Hernandez (C) celebrates with her lawyers
Bayanan hoto, Evelyn Hernández celebrates in court on Monday
An wallafa

Wata kotu a kasar El salvador ta sallami wata mata da a baya aka samu da laifin kisa bayan da tayi barin cikin jaririn da ta ke dauke da shi a shekarar 2016.

Evelyn Hernandez ta fuskanci hukuncin daurin shekara 40 a gidan yari kafin wannan ktun ta yi watsi da hukuncin farko da aka yanke ma ta.

An dai yanke mata wancan hukuncin ne tun tana 'yar shekara goma sha wni abu da haihuwa saboda ta yi barin ciki da ta dauka bayan wani yayi ma ta fyade.

Alkalin da ya saurari sabuwar shari'ar ta Evelyn Hernandez ya fuskanci kalubale biyu:

Salvadorean rape victim Evelyn Hernandez is seen prior to her hearing
Bayanan hoto, Ms Hernández ta dade tana cewa ba ta da laifi

Alkalin ya sallame ta ko kuma ya aika da ita kurkuku na tsawon goman shekaru.

A karshe duk da kokarin da jami'i mai shigar da kara yayi na a mai da ta kurkuku, an sallami matar kuma an wanke ta da laifin kashe jaririn da ta ce ba ma san tana dauke da shi a mahaifarta ba.

Alkain ya kuma yarda da matar da ta ce ba a yi ma ta adalci ba, da aka yanke ma ta hukuncin kisa saboda ta yi bari.

Masu goyon bayan matar sun dade suna cea Evelyn ce ya kamata a nema wa hakki, tun da fyade aka yi ma ta.

Duk da cewa an sallami Evelyn Hernandez, amma akwai mata da dama a El salavador da ke fuskantar tuhuma a kurkukun kasar da laifuka irin nata.

Kuma duk da cewa Shugaban kasar Nayin Bukele mai tsattsauran ra'ayi ne, amma ya nuna aniyarsa ta sassauta dokar kasar ta hana zubar da ciki musamman idan ta shafi lafiyar uwar da ke daule da cikin.