Amurka ta yi gwajin makami mai linzami

Hoton da Fadar tsaron Amurka ta Pentagon ta fitar na gwajin makaim mai linzami ranar 18 ga watan Agustan 2019
Bayanan hoto, Fadar tsaron Amurka ta Pentagon ce ta fitar da hoton gwajin makamin mai linzami
An wallafa

Amurka ta yi gwajin wani makami mai linzami mai cin matsakaicin zango 'yan makonni bayan ficewarta daga wata yarjejeniyar makamin nukiliya da Rasha, wadda ta haramta amfani da makamantansu.

Fadar tsaro ta Pentagon ta ce ta gwada makamin ne kusa da gabar ruwan California a ranar Lahadi.

Rasha ta zargi Amurka da "kara rura wutar rashin jituwa".

Amurkar dai ta fice daga yarjejeniyar Intermediate-Range Nuclear Forces (INF) ranar 2 ga watan Agusta bayan ta zargi Rasha da saba yarjejeniyar, abin da Rashar ta sha musantawa.

Masana na ganin cewa karyewar yarjejeniyar ka iya haifar da rige-rige wajen mallakar sababbin makamai.

Ita dai wannan yarjejeniya ta haramta amfani da makamai masu cin zangon kilomita 500 zuwa 5,500.

Pentagon ta ce makamin da ta gwada daga sansanin sojojinta na ruwa na San Nicolas Island kusa da gabar ruwan Los Angeles, "na yau-da-kullum ne", saboda haka bai kai girman nukiliya ba.

"Makamin ya bar kasa ne sannan kuma ya bugi daidai inda aka harba shi bayan ya shafe sama da kilimita 500 a sama," kamar yadda ma'aikatar tsaron Amurka ta bayyana.

"Bayanan da aka tattara daga wannan gwaji zai bai wa ma'aikatar tsaron damar sake kera wasu makaman masu cin matsakaicin zango."

Ita kuwa Rasha ta kira gwajin da "abin nadama".

An ambato mataimakin ministan harkokin wajen Rashar Sergei Ryabkov yana cewa "Amurka tana yunkurin kara rura wuta ne kawai," saboda haka "ba za mu mayar da martani ga tsokana ba".

Me ya faru da yarjejeniyar?

An zargi Rasha da saba ka'idojin yarjejeniyar a baya. Sai dai a afarkon wannan shekarar Amurka da kungiyar NATO sun ce akwai hujjoji da ke nuna cewa Rashar ta fito da makaman 9M729 masu linzami.

Shugaban kasar Putin ya musanta zargin sannan ya ce kawai Amurka na kokarin amfani da hakan ne domin ta fice daga yarjejeniyar.

A watan Fabarairu Donald Trump ya sanya 2 ga watan Agusta a matsayin wa'adin cewa kasarsa za ta fice idan Rasha ba ta bayar da hadin kai ba.

Makaman Rasha 9M729 masu linzami
Bayanan hoto, Makaman Rasha 9M729 masu linzami suna firgita Amurka da kawayenta

Karyewar yarjejeniyar mai cike da tarihi ya jawo fargabar cewa hakan ka iya haddasa rige-rige tsakanin kasashen Amurka da Rasha da China.

Wacce ce yarjejeniyar?

Mikhail Gorbachev da Ronald Reagan suna saka hannu kan yarjejeniyar INF Treaty a 1987
Bayanan hoto, Shugaban tarayyar Soviet Mikhail Gorbachev da Shugaban Amurka Ronald Reagan suna saka wa yarjejeniyar hannu a shekarar 1987
  • Yarjejeniyar da Amurka da Rasha suka sanya wa hannu ta haramta amfani da makamai masu cin gajere da matsakaicin zango, sai dai wadanda ake iya harbawa daga ruwa
  • Amurka ta damu da makaman SS-20 da Tarayyar Soviet take amfani da su a shekarar 1979, abin da ya sa Amurkar ta jibge makamin Pershing a nahiyar Turai - hakan ya jawo zanga-zanga
  • Zuwa shekarar 1991, kusan makamai 2,700 aka lalata
  • Kasashen biyu sun amince su rika bincika aikace-aikacen junansu game da makaman