Kauracewa kafofin sada zumunta ne babban makami - Phil Neville

Paul Pogba
Bayanan hoto, Golan Wolves Rui Patricio ya buge fenaretin da Pogba ya dauka a wasansu da Manchester United inda aka tashi 1-1
An wallafa

Kocin kungiyar kwallon kafa ta mata ta Ingila, Phil Neville ya ce kamata yayi 'yan kwallo su kauracewa shafukan sada zumunta domin aikawa da sako ga masu cin zarafinsu.

Neville ya fadi wadannan kalaman ne bayan da aka ci mutuncin dan wasan manchester United Paul Pogba a shafukan intanet saboda ya gaza cin wani dukan daga kai sai gola a wasan kungiyar da Wolves ranar Litinin.

Phile Veville ya ce: "Tilas ne mu dauki matakai a matsayinmu na al'ummar da ke wasan kwallon kafa. Na ja layi kan wannan batu daga 'yan wasan da na ke horaswa, kuma na san hukumar da ke kula da kwallon firimiya ma sun ja layi."

Paul Pogba
Bayanan hoto, Paul Pogba

Ya kuma ce "Ina ganin kamata yayi mu daina amfani da shafukan, domin Twitter ba za ta yi wani abu a kai ba, Instagram ma haka - sai dai kawai su aiko maka da sakon imel cewa za su bincike al'amarin amma babu abin da ke sauyawa."