Aston Villa ta yi nasarar farko a Premier

Kwallon da Wesley ya ci Everton
Bayanan hoto, Wesley ya koma Aston Villa daga Bruges a kan fan miliyan 22 a bazara
An wallafa

Aston Villa ta samu makinta uku na farko a gasar Premier ta bana a sanadin kwallayen da Wesley da Anwar El Ghazali suka ci ma ta a wasansu da Everton.

Wesley dan Brazil, wanda ya koma Villa daga Bruges a kan kudin da kungiyar ba ta taba kashewa ba wajen sayen wani dan wasa ya fara tabbatar da sunansa a jerin wadanda suka daga raga a kwallon kafar Ingila, a minti na 21 da shiga fili, bayan da Jota ya ba shi wata bal.

El Ghazi ya ci ta biyu cikammakin kwallayen bayan cikar minti na 90 a wasan, bayan John McGinn ya zura masa bal.

Nasarar ta daga kungiyar ta kociya Dean Smith zuwa mataki na 11 a teburin Premier, kuma ta kasance nasara ta farko a gasar ta Premier da Villa ta yi tun watan Fabrairu na 2016, lokacin da ta ci Norwich 2-0, inda ta yi canjaras 1, aka doke ta sau 14, kuma ba ta ci ko daya ba.

Jota na Aston Villa
Bayanan hoto, Jota ne ya ba wa Wesley bal din da ya fara ci wa Aston Villa

Alex Iwobi wanda ya shigo daga baya ya kusa farke wa Everton lokacin suna 1-0, amma hakarsa ba ta cimma ruwa ba.

Kungiyar Everton ta kociya Marco Silva wadda ta mamaye wasan da farko, ta yi duk abin da za ta iya amma ta gagara cin ko daya, abin da kociyan ya nuna takaicinsa a kai.

Wannan shi ne karo na uku da Everton ta yi rashin nasara a gasar Premier a wasanta 14 na baya inda ta ci 7, ta yi canjaras a 4 ta kuma sha kashi a 3.

Wannan shi ne karon farko da kociyan Aston Villa Dean Smith ya yi nasara a karawa da wata kungiya a Premier.

Saboda a matsayinsa na mai horarwa an doke shi a dukkanin wasa takwas da ya taba jagorantar kungiyoyin Walsall da Brentford da kuma Aston Villa.

Yanzu kenan Everton ta yi rashin nasara a jere a gasar Premier a karawa da sabbin haurowa, inda Fulham ta doke ta ita ma 2-0 a watan Afrilu, a karon farko tun Agusta na 2011.

Wasannin kungiyoyin na gaba:

Aston Villa za ta gidan Crewe a gasar kofin Carabao ranar Talata da karfe 7:45 na dare agogon Najeriya.

Sannan kuma ta tafi gidan Crystal Palace a gasar Premier ranar Asabar 31 ga watan Agusta da karfe 3:00 na rana, agogon Najeriya

Ita kuwa Everton za ta je Lincoln a gasar ta kofin Carabao ne ranar Laraba da karfe 7:45 na dare agogon Najeriya.

Bayan nan ne kuma kungiyar za ta koma wasanta na Premier a gida da Wolves, ranar Lahadi 1 ga watan Satumba da karfe 2:00 na rana agogon Najeriya.