Kacici-kacicin Ranar Hausa ta duniya

Asalin hoton, Getty Images
A ranar 26 ga watan Agustan kowace shekara ce ake gudanar da bikin Ranar Hausa ta duniya.
Shekaru biyar da suka gabata ne wasu fitattun masu amfani da shafukan sada zumunta a Najeriya suka kirkiro da wannan ranar tare da kebe kowace ranar 26 ga watan Agusta a zaman ranar wannan bikin.
Abokin aikinmu Abdulbaqi Jari wanda aka fi sani da Bahaushe a shafukan sada zumunta na daya daga cikin wadanda suka assasa wannan rana, wanda kuma aka nada Sarkin Yakin Hausawan Afirka a raar Litinin.
Ga wannan kacici-kacicin ku latsa ku yi don sanin ko kun kware a harshen Hausa ko da sauranku.
Yadda za a yi jarrabawa: Idan a wayar hannu za a yi sai a taba kalmar Hausa da ke hagu sannan a taba ma'anarta a Ingilishi a bangaren dama.
A kwamfuta kuma za a danna kalmar Hausa ne a bangaren hannu, sannan a je a danna ma'anarta a bangaren dama.























