Yadda annobar korona ta jefa 'yan ci-rani cikin ƙunci a duniya

Asalin hoton, Getty Images
Dubban 'yan ci-ranin Afrika ne suka makale a hanya - sun kasa isa inda za su ko kuma su koma gida saboda annobar cutar korona ta janyo komai ya tsaya cik a duniya.
Hanyoyi biyu garesu na ficewa: ta arewacin Africa ta Gabar Tekun Aden zuwa Gabas ta Tsakiya da kuma ta Bahar Rum daga Libya zuwa nahiyar Turai.
Hanyar da ake bi ta arewacin Afrika, Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ci-rani (IOM) ta ce an samu matukar raguwa a 'yan ci ranin da ke fita daga nahiyar.
A watan Afrilu, 'yan ci-rani 1, 725 ne kawai suka isa Yemen daga arewacin Afrika, idan aka hada da 'yan ci-rani 7, 223 a watan Amaris da 9, 624 a watan Fabrairu da 11, 101 a watan janairun bana.
A bara kawai, sama da mutane 138,000 ne suka tsallaka Yemen a cikin kwale-kwale, mafi yawansu 'yan Habasha da ke niyyar shiga Saudiyya neman aiki.
A tashar jirgin ruwa ta Bosaso da ke Somaliya, 'yan ci-ranin da ke niyyar shiga Gabas ta Tsakiya sun makale.
'Cutar korona ta sauya komai'
IOM ta yi kiyasin cewa kusan 'yan ci-rani 400 ne a halin yanzu, wasu al'ummun Habasha suka bai wa mafaka a unguwannain da aka gin aba a bisa ka'ida ba a birane, amma hukumar ta ce suna fuskantar tsangwama da cin zarafi saboda ana ganin cewa matafiya na dauke da cutar.
Wani dan ci-rani mai shekaru 19 ya shaida wa IOm cewa: "Watana uku a nan. Cutar korona ta sauya komai. Ba zan iya ci gab aba kuma b azan iya komawa inda na fito ba saboda an rufe duka iyakoki."
A Djibouti, daruruwan 'yan ci-rani ne masu safarar mutane suka yi watsi da su a kasar da ke wadanda annobar ta fi muni a Afrika.
A halin da ake ciki, a tsallaken Bahar Maliya a Saudiyya da Hadaddiyar Daular larabawa an dawo da 'yan ci-ranin kasar Habasha kusan 3,000 a jiragen saman daukar kaya bisa zargin cewa suna dauke da cutar korona.
Mafi yawansu ma'aikata ne a gidajen mutane - ciki har da masu shara da wanke-wanke - wadanda ke aiki bisa ka'ida a kasashen yankin Larabawa mai arzikin main fetur.
A Libya - daya daga cikin hanyoyin da suke bi su fice, kuma teku mafi hadari a balaguron 'yan ci-rani - an sa dokokin da suka hana kwale-kwalen agaji ceto 'yan ci-ranin da suka makale a teku - inda ake tilastawa 'yan ci-ranin komawa kasarsu mai cike da rikici.

Asalin hoton, AFP
Akwai yiwuwar cewa za a samu karuwar masu kokarin shiga Turai ci-rani da zarar an dage dokokin hana zirga-zirga - ba don komai ba sai don kulle a kasashen Afrika ya kara ruruta talauci kuma ya janyo tattalin arzikin kasahen ya kara durkushewa.
Ga kasashen Turai kuwa, sun yi amfani da annobar cutar korona wajen sake siyasantar da batun ci-rani.
Kasar Malta ta rufe tashoshin jirgin ruwanta kuma ta mayar da 'yan ci-rani Libya, yayin da Italiya ta ce za a killace 'yan ci-rani a cikin jiragen ruwan ceto.
Cutar korona ta bankado cewa 'yan ci-rani ne mutanen da aka fi nuna wa wariya a lokacin wannan annobar.
Hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce cikin kasashe 167 da suka rufe iyakokinsu gaba daya ko rabi-da-rabi don shawo kan annobar, 57 ba su yi wani tanadi ga mutanen da ke neman mafaka ba.
Hakkin neman mafaka hakkin bil Adam na, duk da cewa a shekarun baya-bayan nan kasashe da dama sun nemi su takaita shi.
There is likely to be a sharp rise in attempts to migrate to Europe once travel restrictions are lifted, not least because lockdowns have worsened poverty in Africa'
Mafi yawan 'yan ci-ranin Afrika na tsayawa ne a Afrika
A Turai, kasashe kamar Austria, da aka dade da sanin cewa suna da manufofi masu tsauri kan ci-rani, sun dakatar da bayar da hakkin neman mafaka kuma sun yi amfani ne da cutar Covid-19.
Ba wai hakkin 'yan ci-rani kawai aka taka ba, ana dora masu laifi, an samu karuwar nuna kin jinin baki saboda ana dora wa 'yan ci-rani cutar kuma 'yan siyasa da 'yan jarida na nuna masu wariya.
A birnin Guangshou da ke China, an kori 'yan ci-ranin Afrika daga gidajensu na haya, kuma an wulakanta su sannan an tilasta masu killace kansu saboda fargabar cutar korona, da kuma wariyar launin fata - wannan ya janyo bacin rai a Afrika.
Mafi yawan ci-rani a Afrika acikin nahiyar yake - 'yan Zimbabwe a Afrika ta Kudu, 'yan ci-ranin Sudan ta Kudu a Uganda da ma'aikata 'yan Burkina Faso a Kwaddebuwa.
Afrika ta Kudu c eke da mafi yawan masu dauke da cutar korona a Afrika kuma yanki ne da miliyoyin 'yan ci-rani ke muradin shiga.
Gwamnati ta dade tana so ta rage ci-rani, kuma ta yi amfani da wannan damar da annobar ta haifar wajen gina Katanga a iyakarta da Zimbabwe.
Akwai hadarin cewa Covid-19 zai yi mummunan tasiri ga hakkokin 'yan ci-rani, yayin da kasashe ke ci gaba da aiwatar da manufofin da za su hana mutane neman na sa wa a bakin salati a Turai, da ma wadanda ke tserewa bita da kullin siyasa.






























