Hotunan abubuwan da suka faru a Najeriya cikin makon nan 24-29 ga Mayun 2020

An wallafa

Wasu zababbun hotunan abubuwan da suka faru a Najeriya a makon nan 24-29 ga Mayun 2020.

Wasu Musulmai kenan a jihar Ogun da ke Kudu maso Yammacin Najeriya inda suke gudanar da Sallar Idi duk da shawarwari da gwamnatin ƙasar ta bayar ga jama'a na su yi sallah a gida.
Bayanan hoto, Wasu Musulmai kenan a jihar Ogun da ke Kudu maso Yammacin Najeriya inda suke gudanar da Sallar Idi duk da shawarwari da gwamnatin ƙasar ta bayar ga jama'a na su yi sallah a gida.
Wasu tarin takalma a wajen wani masallaci da ke jihar Ogun. Mutanen sun shiga cikin masallacin ne domin gudanar da sallar Idi.
Bayanan hoto, Wasu tarin takalma a wajen wani masallaci da ke jihar Ogun. Mutanen sun shiga cikin masallacin ne domin gudanar da Sallar Idi.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da wasu maƙarrabansa a yayin da suke gudanar da Sallar Idi a ranar Lahadi
Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da wasu maƙarrabansa a yayin da suke gudanar da Sallar Idi a ranar Lahadi.
Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum tare da Shehun Borno Abubakar Ibn Umar Garbai a yayin da suke gudanar da Sallar Idi a ranar Lahadi.
Bayanan hoto, Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum tare da Shehun Borno Abubakar Ibn Umar Garbai a yayin da suke gudanar da Sallar Idi a ranar Lahadi.
Sallar Idin Sabon Sarkin Kano ta farko tare da gwamna
Bayanan hoto, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi Sallar Idi a karon farko a matsayinsa na sabon Sarkin Kano tare da gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kenan yayin da yake tattaunawa da gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal kan matsalolin tsaron da jihar Sokoto ke fama da su a halin yanzu.
Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kenan yayin da yake tattaunawa da gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal kan matsalolin tsaron da jihar Sokoto ke fama da su a halin yanzu.
Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila yayin da ake duba yanayin zafin jikinsa kafin ya shiga harabar majalisar ƙasar a ranar Alhamis.
Bayanan hoto, Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila yayin da ake duba yanayin zafin jikinsa kafin ya shiga harabar majalisar ƙasar a ranar Alhamis.
Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle kenan a gidansa da ke Maradun yayin da yake bayar da takardar kama aiki ga sabon Sarkin Kauran Namoda Mai Grima Sanusi M. Asha.
Bayanan hoto, Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle kenan a gidansa da ke Maradun yayin da yake bayar da takardar kama aiki ga sabon Sarkin Kauran Namoda Mai Grima Sanusi M. Asha.