#WeAreTired: Yadda matan Najeriya suka yunƙuro don kawar da matsalar fyaɗe

Asalin hoton, Uwavera Omozuwa/facebook
- Marubuci, Daga Nduka Orjinmo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Lagos
- An wallafa
Dubban mutane ne a Najeriya suka fusata sakamakon kisan wata yarinya 'yar jami'a mai shekaru 22. An kashe ta ne a wata coci da ke kusa da jami'ar Benin a jihar Edo.
Iyayen Uwavera Omozuwa sun ce an yi wa 'yarsu fyaɗe sa'annan aka yi mata kisan gilla.
Wannan na ɗaya daga cikin abubuwan da suka tayar da hankali a ƙasar har hakan ya jawo zanga-zanga da kuma yin kiran daukar mataki a kafafen sada zumunta musamman a Twitter inda ake amfani da maudu'i'n #WeAreTired.
'Yan Najeriya da dama na zargin tsarin shari'ar ƙasar inda suke cewa zai yi wuya a yanke wa mutum hukunci mai tsauri idan ya yi fyaɗe kuma a karshe sai a ɗora wa matan laifi.
Gargaɗi: Wannan maƙalar na ɗauke da bayanai masu tayar da hankali

A karon farko da aka ci zarafin "Wanda Ebe" mai shekaru 36, ba ta kai shekaru shida da haihuwa ba.
Ta bayyana cewa mai kula da ita -- wadda ta mata ce mai matsakaitan shekaru -- ta rinƙa tilasta mata lasar al'aurarta idan suka kaɗaita su biyu.
A lokacin da take shekaru shida, ƴunƙurin da Ms Ebe ta yi na kai ƙarar mai kula da ita wurin iyayenta ya kusan kai wa ga rasa ranta.
"Ta watsa mini bokiti guda na ruwan zafi a kaina wanda hakan ya sa na ƙone matuƙa. Dole aka kai ni asibiti abin da ya sa na shafe shekara ɗaya ban je makaranta ba".
Ms Ebe ta bayyana cewa mai kula da ita ta shaida wa iyayenta cewa kuskure ne ya sa ta kwara wa 'yarsu ruwan zafi.

Asalin hoton, Wanda Ebe
A karo na biyu kuma da aka ci zarafin Ms Ebe tana da shekaru 21, a lokaci tana aji biyu a jami'a. Ta bayyana cewa ba ta daɗe da warkewa daga wata tiyata da aka yi mata ba.
Ta kara da cewa wani likita ne ya yi mata fyaɗe wanda ya fake da cewa zai duba lafiyarta a gidansa a maimakon asibiti.
"Ya yaga mini tufafi ya yi mini fyaɗe," a cewar ta. "Ba ni da kuzari sakamakon tiyatar da aka yi mini, ba yadda na iya domin na hana shi."
"Ban je wurin 'yan sanda ba ko wani ba kan wannan lamari. Ban ma san cewa za a iya kai ƙarar wanda ya yi fyaɗe ga 'yan sanda ba."

- Idan an taɓa cin zarafin ku ko fyaɗe a Najeriya, za ku iya tuntuɓar hukumar at Naptip.

Wurin da ake shan wuya kafin samun mai fyaɗe da laifi
A Najeriya, ba wai sabon abu ba ne idan an yi fyaɗe a ƙi kai ƙara ga 'yan sanda.
Wasu da abin ya shafa da iyalansu na tsoron tsangwama, ko cin kuɗinsu da 'yan sanda za su yi, ko kuma rashin yarda da tsarin shari'ar ƙasar, wanda hakan ya sa ba su so su kai ƙara.
Akwai kuma wasu lokutan da ake samun wasu da ke zuwa su kai ƙara idan an yi fyaɗe, amma ƙarshe sai a yi ta yi musu mugayen kalamai a ofishin 'yan sanda.
Zargin 'yan sanda da yi wa mata fyaɗe
A 2019, wasu mata a birnin tarayyar Najeriya Abuja sun yi zargin 'yan sanda da yi musu fyaɗe yayin wani samame da 'yan sandan suka kai.
Matan sun bayyana cewa 'yan sandan sun zarge su da laifin karuwanci, ko da 'yan sandan suka kai su ofishin su, matan sun bayyana cewa 'yan sandan sun yi musu fyaɗe a lokuta daban-daban.
'Yan sandan sun musanta zargin da ake yi musu, amma duk da haka wannan shari'ar na kotu.

Ɗaya daga cikin mai kare matan Dorothy Njemanze ta shaida wa BBC cewa "Irin waɗannan lamuran ba su bai wa mutane ƙwarin gwiwar cewa ofishin 'yan sanda wuri ne da mutum zai iya samun taimako".
Babu wata ƙididdiga da za ta nuna yawan fyaɗen da ake yi a ƙasashen Yammacin Afirka a duk shekara. Sai dai a Hukumar Ƙididdiga ta Najeriya ta bayyana cewa an samu rahotanni kan fyaɗe a 2017 sama da 2,200.
Sai dai masana sun bayyana cewa akwai yiwuwar yawan ya wuce hakan.
Ms Njemanze ta bayyana cewa "a duk mako muna samun a kalla rahotanni 6 kan cin zarafi". "Lokacin kullen nan na korona, mun rinƙa samun rahotanni huɗu zuwa bakwai a duk rana kuma kashi 70 a cikin su na da alaƙa da fyaɗe."
Ba a aiwatar da sabbin dokoki ba
A wani bincike da aka gudanar a 2019, ya nuna cewa kashi ɗaya bisa uku na mata a Najeriya sun taɓa fuskantar akalla wani na'u'i na cin zarafi zuwa lokacin da za su kai shekaru 25.
Dokokin da aka yi a 'yan kwanakin nan sun sa an ƙara faɗaɗa dokokin fyaɗe inda za a iya hukunta waɗanda suka yi fyaɗe a Najeriya.
"A baya dai, sashen kundin tsarin mulkin Najeriya da ke da alaƙa da fyaɗe na ƙarƙashin sashen laifuka kuma ya bayyana cewa shari'o'i masu alaƙa da fyade dole ne a yi su cikin watanni biyu ko kuma ba za a ci gaba da saurarensu ba, amma a halin yanzu an sauya haka," in ji Stephanie Ekpebulu, wata lauya mai taimaka wa waɗanda aka yi wa fyaɗe.
Don't take your bath, don't discard clothing or anything that could be evidence."
Sai dai jihohi da dama a Najeriya ba su aiwatar da waɗannan sabbin dokokin ba.
Matsalolin da ke tattare da tsarin shari'a a Najeriya ke sa wa a shafe shekara da shekaru ana yin shari'a daya, kuma 'yan sanda ba su gudanar da bincike yadda ya kamata, wanda hakan ke sa waɗanda aka zalunta su guji zuwa kotu.
Ms Njemanze ta bayar da shawara ga duk wadda aka yi wa fyaɗe da ta yi ƙoƙari ta tanadi hujjoji, kamar kaya da za a iya bayar da shaidar su a kotu.
"Sau da dama asibitoci kan so ganin rubutaccen rahoto daga 'yan sanda kafin su duba wadda aka yi wa fyaɗe, wannan ba daidai bane sakamakon lokaci kan iya ƙurewa ba tare da an samu shaidar da ake so ba," in ji ta.
"Abu na farko da ya kamata a yi shi ne a samu duk wata hujja da ake buƙata sa'annan a yi magani da zai kare mace daga ɗaukar duk wata cuta da ake ɗauka ta hanyar saduwa.
Karin labarai da za ku so ku karanta:



























