Ƙayatattun hotunan abubuwan da suka faru a duniya makon jiya

An wallafa

Zababbun hotunan labarai da aka dauka a fadin duniya a makon jiya.

Wata mata na ihu bayan an watsa mata barkonon tsohuwa
Bayanan hoto, Wata mata da 'yan sanda suka watsawa barkonon tsohuwa a yunkurin tarwatsa masu zanga-zangar adawa da sabuwar dokar tsaro kan Hong Kong.
Wani mutum yana tumbuke butun butumin sarki Belgium Leopold na biyu
Bayanan hoto, Wani mutun mutumin sarki Belgium Leopold II da aka tumbuke a garin Ghent, a yayin bikin shekara 60 da samun 'yancin kan Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo
Wani yaro dauke da jirgin leda da aka kera shi kamar fatalwa
Bayanan hoto, Wani yaro dauke da jirgin leda da aka kera shi kamar fatalwa a kauyen Depok, da ke wajen Jakarta, babban birnin Indonesia.
Wata mai ninkaya zagaye da ledoji da robobi
Bayanan hoto, Daya daga cikin manyan masu ninkaya a Turkiyya Sahika Encumen da ta yi nutso a tekun Bosphorus domin wayar da kan al'umma game da illar da leda da robobi ke yi wa teku
Wasu manoma da ke kokarin korar fadin ɗango da suka mamaye inda suke
Bayanan hoto, Wasu manoma da ke kokarin korar farin-ɗango da suka mamaye inda suke a wajen garin Sukkur a Pakistan. Kasar ta sanya dokar ta baci, tana cewa wannan gungun farin shi ne mafi muni da ake gani cikin sama da shekara 40
People dine at a 500m-long table on Charles Bridge
Bayanan hoto, Mutane sun fito cin abinci a kan gadar nan ta Charles da ke da tsawon mita 500, bayan an sassauta dokar kulle a birnin Prague
'Yan makaranta sanye da takunkumin fuska a zaune cikin tsohuwar takardar zabe an raba su da zimmar bada tazara tsakaninsu
Bayanan hoto, Dalibai a lardin Pathum Thani zaune a teburan da aka yi da akwatunan zaben da aka gama amfani da su domin hana su cakuduwa, bayan an sake bude makarantu a Thailand
Ginin Empire da ke birnin New York an kunna masa fitila mai launin bakan gizo
Bayanan hoto, Ginin Empire da ke birnin New York an kunna masa fitila mai launin bakan gizo domin murnar hutun karshen mako
Damisa na hamma
Bayanan hoto, Wata damusa na hamma, bayan sake bude gidan namun daji na Edingurgh
Yarima Charles na kallon wata tsuhuwar alade
Bayanan hoto, Yarima Charles na kallon wata tsohuwar macen lade yayin wata ziyara da ya kai gonar Cotswold da ke kusa da Cheltenham a yammacin Ingila

Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka.