Daniel Lewis Lee: Za a zartar da hukuncin kisa a Amurka karon farko cikin shekara 17

Daniel Lewis Lee
Bayanan hoto, Lee ya kashe wasu mutum uku iyalan gida ɗaya kafin daga baya ya jefa gawarwakinsu cikin wani kududdufi
An wallafa

A karon farko cikin shekara 17 a Jihar Indiana, Amurka za ta yanke hukuncin kisa kan wani ɗan ƙasar bayan wata kotun ɗaukaka ƙara ta umarci yin haka.

An yanke wa Daniel Lewis Lee da wani mai taimaka masa hukuncin kisa saboda kashe wasu mutum uku iyalan gida ɗaya a shekarar 1996.

Wasu ƴan uwan waɗanda Daniel Lewis Lee ya kashe sun nemi a jinkirta kashe shi saboda annobar korona.

Sai dai umarnin kotun na nufin za a yanke hukuncin ta hanyar yi masa allurar guba ke nan.

Kotun Kolin ta ƙi amincewa da hukuncin da wata ƙaramar kotu ta yanke da ta dakatar da yanke hukuncin kan Lee mai shekara 47 da haihuwa. inda ta ce babu wata dokar jiha ko ta tarayyar ƙasar da ta bai wa ƴan uwan waɗanda aka kashe damar halartar yanke hukuncin.

Ƴan uwan wadanda aka kashe ɗin na iya ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙolin Amurka amma dole Kotun Kolin ta ɗauki matakin kafin ƙarfe 4:00 agogon Indiana idan tana son dakatar da yanke hukuncin, inji Jaridar New York Times.

An shirya yanke hukunci kan Lee ne a watan Disamba, sai dai an samu jinkiri bayan da kotun ta hana ɗaukar matakin.

Earlene Peterson, mai shekara 81 - wadda Lee ya kashe ƴarta da jikarta da mijin ƴar tata - na adawa da yanke masa hukuncin kisa.

Ta so a yanke ma sa hukuncin daurin rai-da-rai ne.

A yanzu an shirya yanke hukuncin kisan kan Lee tare da wasu mutum uku da za a yi a watan Yuli da Agusta. Dukkan mutanen na fuskantar hukuncin kisa ne saboda sun kashe ƙananan yara.

A bara, gwamnatin Shugaba Donald Trump ta ce za ta ci gaba da yanke hukuncin kisa bayan da aka daɗe da jinkirta yin haka.

A wancan lokacin, sakataren shari'a na Amurka William Barr ya ce: "Ma'aikatar Shari'a na son a ci gaba da yanke hukuncin kisa kan masu aikata munanan laifuka".

Amma wasu masu adawa da matakin sun soke shi, inda suke cewa akwai dalilai na siyasa, kuma sun ce ana iya gaggauta yanke hukunci maimakon a bi a sannu.

Mutum na karshe da aka yanke wa hukuncin kisa shi ne Loius Jones Jr mai shekara 53, wanda tsohon soja ne da ya yi yakin Gulf bayan da ya kashe Tracie Joy McBride, wata soja mai shekara 19.

Bambanci tsakanin shari'ar jiha da ta gwamnatin tarayya

A ƙarƙashin dokar Amurka, akwai laifuka iri biyu - akwai laifin da ke ƙarƙashin hurumin gwamantin jiha ko na yanki, da wanda ke ƙarƙashin hurumin gwamnatin tarayya.

Laifuka kamar yin jabun kuɗi ko satar kaddarori ta hanyoyin sadarwa na karkashin hurumin gwamnatin tarayya ne.