Iran ta boyewa duniya yawan ainihin wadanda cutar korona ta kashe

Gwamnatin kasar ta sha musanta boye ainihin wadanda cutar ta kama a kasar da ma wadanda ta kashe.
Bayanan hoto, Gwamnatin kasar ta sha musanta boye ainihin wadanda cutar ta kama a kasar da ma wadanda ta kashe.
An wallafa

Wani binciken BBC ya gano cewa ainihin adadin wadanda cutar korona ta kashe a Iran ya ninka wanda hukumomin kasar suka sanar har sau uku.

Mahukunta dai sun ce mutum dubu goma sha hudu cutar ta kashe tun bayan bullar ta har zuwa wannan lokaci, sai dai kunshin bayanan da BBC ta samu daga wurin wani mai tonon silili sun nuna cewa akalla mutum dubu arba'in da biyu ne suka mutu sakamakon cutar a kasar.

Wani Karin bayani da ya bayyana kuma shine mutum na farko da cutar ta kashe ya mutu ne a watan Janairun wannan shekara, wato wata daya kafin lokacin da hukumomin kasar suka sanar.

Gwamnatin ta sha musanta boye ainihin bayanan wadanda cutar ta kama a kasar da ma wadanda ta kashe.

Iran na daya daga cikin kasashen da cutar ta fi tafka ta'adi a ciki.
Bayanan hoto, Iran na daya daga cikin kasashen da cutar ta fi tafka ta'adi a ciki.

Sannan adadin wadanda suka kamu ya kai mutum 451,024, sabanin 278,827 da gwamnati ta sanar.

Kasar na daya daga cikin kasashen da cutar ta fi tafka ta'adi a ciki.

Tun bayan barkewar cutar a Iran kwararru ke jefa ayar tambaya a kan irin bayanan da hukumomin kasar ke bayarwa, na wadanda suka kamu, da wadanda suka mutu, da kuma wadanda ke warkewa a kowacce rana.

Su kansu alkalumman da gwamnati a matakin tarayya ke bayarwa sun rika cin karo da wadanda hukumomin lardunan ke bayarwa.

Hotunan wasu da cutar ta kashe a Iran
Bayanan hoto, Hotunan wasu da cutar ta kashe a Iran

Birnin Tehran ne ya fi yawan wadanda suka mutu da mutum dubu takwas da dari da ashirin.

To sai dai mutane dubu daya da dari tara da goma sha shidda cikin wadanda suka mutun ba yan kasar ba ne, domin yawancin su 'yan cirani ne da 'yan gudun hijira da ke shiga kasar daga Afghanistan.

A kwanakin baya ma an gano wani jirgin kasar da ya tashi zuwa kasashe da dama duk da cewa an sanya dokar hana jigila a kasashen.

BBC ta samu bayanai masu nuna cewa kamfanin jirgin saman ya karya doka, sannan zai iya yada cutar.