Cutar Polio: An bai wa Afrika shaidar rabuwa da Polio

Polio
An wallafa

Wata hukuma mai zaman kanta dake bayar da shaidar rabuwa da Polio a Afirka ta bayyana cewa nahiyar ta rabu da kwayar cutar ta polio dake watsuwa a cikin al'umma.

Kwayar cutar tana kama yara ne 'yan kasa da shekara biyar, inda a wasu lokutan take nakasa su. A wasu lokutan a kan rasa rai idan har ta kama gabobin numfashi.

Shekara 25 da ta gabata, cutar ta nakasa dubban yara 'yan Afirka.

A yanzu kasashen Afghanistan da Pakistan ne kawai ke fama da cutar a duka fadin duniya.

Polio ba ta da magani, amma riga-kafin da ake digawa yara a baki na ba da kariya.

Najeriya ce kasa ta karshe a nahiyar Afirka da ba a ayyana ta rabu da cutar ta polio mai watsuwa ba, da a turance ake cewa Wild Polio, kasancewar shekara goma da ta gabata fiye da rabin masu dauke da cutar a duka fadin duniya a Najeriya suke.

Polio

A yanzu fiye da shekaru uku ba a samu ko da yaro daya da ya kamu da ita ba, yayin da aka kwashe shekaru da dama ana aikin riga-kafi.

Kafin yanzu dai sai da jami'an hukumar Lafiya ta Duniya WHO suka ziyarci Najeriya domin tantance ayyukan da kasar ta yi. Muddin aka ba Najeriya shaidar, to a duniya baki daya zai kasance saura kasashen Afghanistan da Pakistan masu cutar.

Da ma kasashen Najeriya da Afghanistan da Pakistan ne suka rage a duniya masu wannan nau'in a duniya a cewar WHO, amma kusan shekaru hudu ke nan Najeriya ba ta sake samun shi wannan nau'in ba abinda ya kawo ta ga matakin na gab da samun shaida rabuwa da ita.

Polio

A tsakiyar wannan shekarar ne dai dama Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce ta amince da takardun neman shaidar rabuwa da cutar shan-Inna wato Polio da kasashen Najeriya da Kamaru da Sudan ta Kudu da kuma Jamhuriyyar Tsakiyar Afirka suka gabatar mata.

WHO ta ce takardu da kuma bayanan da kasashen na Afirka suka gabatar sun cika dukkan sharudan ayyana su a matsayin wadanda ba su da cutar polio, amma dai ana bukatar karin bitar yanayin da suke ciki kafin a bayar da sanarwa ta karshe kan matsayinsu game da cutar mai nakasa yara.

WHO ta ce wannan wani lokaci mai cikke da tarihi ga Afirka da kuma yunkurin kawar da cutar ta Shann Inna daga doron kasa.

Sai dai kuma Hukumar bayar da shaidar rabuwa da polio ta Sashen Afirka za ta sake duba bayanan da kasashen suka gabatar, ana kuma sa ran hukumar bada shaidar mai zaman kanta ta zata bai wa nahiyar Afirka shaida ta rabuwa da polio a cikin watan Agusta, bayan an kammala tsare-tsaren masu wuyan sha'ani.

Muddin a karshe aka ayyna Afirka a matsayin wadda ta rabu da cutar polio, haka zai kasance wata muhimmiyar gaba a yunkurin kawar da cutar a fadin duniya.

Short presentational grey line

A watan Agustan 2019 ne dai Najeriya ta cika shekara uku ba tare da samun wani mai dauke da kwayar cutar polio ba.

Wannan ranar dai tana da muhimmancin gaske kasancewar a tsarin hukumar lafiya ta duniya (WHO), dole sai kasa ta shafe shekara uku ba tare da kamuwa da cutar ba kafin a iya ayyana ta a matsayin wacce ba kwayar polio a cikinta.

To sai dai dole sai WHO ta gudanar da bincike domin tabbatar da lamarin kafin ta iya bayyana cewa ba a samu bullar cutar a cikin shekaru uku ba a kasar.

A shekarar 2012, Najeriya na da a kalla mutum 223 da suka kamu da polio wato rabin adadin wadanda ke da polio duk duniya kenan a cewar WHO.

Kwararru dai sun alakanta wannan nasarar da raguwar rikice-rikice da ake yi da mayakan kungiyar Boko Haram.

Rikicin da ake yi da kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya ne ya sa magunguna ba sa isa wasu yankunan jihar Borno.

Borno dai ita ce jiha wacce aka fi samun mutanen da suka kamu da Polio. A ranar 21 ga watan Augustar shekarar 2016 ne aka samu mutum na karshe wanda ya kamu da polio.

Bayanan bidiyo, Yadda masu cutar Polio suke ji kan ayyana Najeriya kasa maras cutar Polio