Juyin mulkin Mali: Sojoji a Mali sun saki tsohon Shugaba Ibrahim Boubakar Keita

Asalin hoton, Reuters
Sojojin Mali da ke mulkin ƙasar sun saki Tsohon Shugaban ƙasar Ibrahim Boubakar Keita.
An kama Shugaba Keita ne dai a makon da ya gabata bayan ya yi murabus sakamakon tilasta masa da sojojin ƙasar suka yi ya ajiye mulki.
Sai dai har yanzu babu wani tabbaci kan ko za a ci gaba da tsare tsohon shugaban a gidansa.
An hamɓarar da gwamnatin ƙasar ce sakamakon rashin gamsuwa da 'yan ƙasar suka yi kan yadda Shugaba Keita ke tafiyar da mulkinsa, musamman kan yadda tattalin arziƙin ƙasar ya shiga wani hali, da kuma gazawar Mista Keita wurin daƙile masu iƙirarin jihadi a ƙasar.
Sakin Mista Keita na daga cikin manyan abubuwan da wakilan da ƙungiyar ECOWAS da wasu ƙungiyoyi na duniya suka buƙata, ciki har da Tarayyar Turai.
Masu shiga tsakani daga Ƙungiyar ECOWAS a Mali sun bayyana cewa sojojin da suka yi juyin mulki a ƙasar na son ci gaba da mulki har na shekara uku.
Sai dai wakilan ƙungiyar ta ECOWAS ta bayyana cewa sun shaida wa shugabannin gwamnatin riƙon ƙwarya a ƙasar cewa kada su wuce shekara ɗaya suna mulki a ƙasar.
Da ma Mista Keïta ya fuskanci tarzoma daga wurin 'yan kasar gabanin kama shi kuma wasu 'yan kasar ta Mali sun yi maraba da cire shi.
Dubun dubatar mutane sun taru a dandalin Independence da ke Bamako suna busa sarewa, inda wasu suka rika cewa sun yi nasara kan tsohon shugaban kasar.




























