Yadda rikicin El-Rufai da NBA ya ta da tsohon liƙin da ke jikin ƙungiyar lauyoyin Najeriya

Lauyoyin Najeriya
An wallafa

Kungiyar Lauyoyin Najeriya ta samu baraka, kasancewar wasu daga cikin ƴaƴanta sun sanar da yi ma ta kishiya, wadda suka raɗa ma ta suna "Sabuwar Kungiyar Lauyoyin Najeriya."

Ƴan "Sabuwar Kungiyar Lauyoyin Najeriyar" sun yi zargin cewa matsalar bambancin addini da kabilanci da kuma bangaranci suka tilasta musu kafa kungiyar tasu.

Kungiyar Lauyoyin Najeriyar ta fada cikin rudani ne bayan ta janye wata gayyatar da ta yi wa gwamnan jihar Kaduna a matsayin mai jawabi a wajen babban taron da ta yi a makon da ya wuce.

Duk da cewa fushin wasu `ya`yan kungiyar lauyoyin Najeriyar ya fito fili ne har aka ji kansu da uwar kungiyar, sakamakon janye goron gayyatar da ta yi wa gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, ƴan sabuwar kungiyar Lauyoyin, kamar yadda suka zana ma ta suna, sun bayyana cewa matsalar da ta saka su kafa kungiyar ba ta yau ba ce.

Barrister Sulaiman Lere na cikin jigoginta: "Mun shekara sittin ke nan da gudanar da wannan kungiya ta lauyoyi mai manufofi iri ɗaya. Sai dai matsololi sun shige ta da suka haɗa da ƙabilanci da maganar addini da ɓangaranci da rashin ganin daraja da mutuncin juna, maimakon haɗa kan al'umma."

Ya kara da cewa, "muna gani lokaci ya yi bayan mun zauna tare cikin kafa wannan ƙungiya shekara 60 mu kafa sabuwar ƙungiya."

Barrister Sulaiman Lere ya bayyana cewa sabuwar kungiyar tana da magoya baya daga kowane bangaren Najeriya, kuma za su bi dukkan matakan da suka dace wajen ganin kungiyar ta tsaya daram.

Barrister, Sa`idu Tudunwada na goyon bayan wannan yunkurin.

Ya ce: "A shekaru da yawa da suka shuɗe ana nuna bambancin addinin da ƙabilanci da ɓangaranci da kuma nuna ƴan mowa da ƴan bora a cikin tafiyar da ƙungiyar ke yi."

'Darewar ƙungiyar lauyoyin abin takaici ne'

Amma dattawan kungiyar irin su Farfesa Muhammad Tabi`u na jami`ar Bayero ta Kano ya ce abin takici ne rashin adalcin da aka yi da ya sa wasu fita daga kungiyar, kuma babu alheri a cikin darewar kungiyar:

Darewar ƙungiya kamar NBA, a ce kowa ya kama gabansa babu abin da zai jawo sai gurgunta ita ƙungiyar kan tafarkin da aka gina ta a kansu."

Ya ce a ganinsa kamata yayi a sami shugabanni su shiga tsakani domin sasanta mabobin ƙungiyar.

Sai dai Shugaban kungiyar Lauyoyi ta kasa, Olumide Akpata ya nuna cewa akwai a gabansa na dinke kungiyar.

"Na fahinci cewa wannan hakkin yana wuyanmu. Za mu tuntubi `yan kungiyar tamu domin mu maida hankali wajen karfafa ta. Ba na jin cewa akwai alheri a cikin rarrabuwarmu. Saboda haka ina tabbatar muku cewa zan yi bakin kokarina wajen ganin kungiyar lauyoyin Najeriya ta ci gaba da kasancewa dunkulalliya," in ji shi.

Duk da cewa ƴan sabuwar kungiyar lauyoyin na ikirarin cewa ta kasa baki daya ce, tuni wasu ke mata kallon ta arewacin Najeriya ce, kuma alamu na nuna cewa shiyyar kudu masu yamma da kudu maso gabashin kasar su ma sun fara tunanin ballewa, lamarin da ke nuna cewa dinke barakar ba karamin aiki ba ne.