Kar ki bari masu sukar halittarki su karya miki gwiwa

Asalin hoton, Tiktok @summerkmorgan / @danieledriusso / BBC
Bari mu gaya wa kan mu gaskiya, yana da matuƙar wahala ki kauce wa haɗa kanki da abin da waɗansu ke yi - indai har kina shiga shafukan sada zumunta, kina ganin kyawawan mutane a kan wayarki a kowace rana.
Amma a yanzu akwai wata fafutuka da aka fara tana kuma yin tashe a shafukan TikTok da Instagram, wacce ke mayar da hankali kan yin la'akari da aikin da jikinki ya ke miki maimakon kyawun da ya ke sa ki.
''Maimakon ki ce 'wannan duk tsoka ce da kitse a jikin munanan hannayen da ake ɓoyewa... gara kawai ki ce waɗannan hannayen mutum ne. Suna iya ɗaga kaya ko ajiyewa,'' a cewar Erynn Chamber, wadda ke ɗaya daga cikin waɗanda suke aiki da fafutukar a tsawon shekaru, da aka fi sani barin jiki yadda Allah Ya yi shi.
Wataƙila kun ji labarin tsarin alfahari da halittar da kowa ke da ita, wanda ke ƙarfafa wa mata da maza masu ƙiba gwiwa, da kuma tunƙaho da dukkan tsarin jiki, ba tare da duba da yanayin girmansa ko jinsi da ƙabilar da mutum ya fito da yadda yanayin jikin yake ba.
Amma Erynn ta ce ta hanyar bin tsarin alfahari da halittar da kowa ke da ita, ba sai ka je kana ma wani bayanin cewa ''waɗannan ne hannaye mafi kywau da ban taɓa ganin irin su ba a rayuwata.''

Asalin hoton, TikTok / @rynnstar
Me ake nufi da alfahari da halittarka ta ainihi?
Fafutukar alfahari da tsarin halitta yana mayar da hankali ne kan muhawarar da ake yawan yi a kan alfahari da kyan jiki ko jin kunyar rashin kyawun jiki, a cewar Erynn.
"A wasu lokutan muna samun wannan matsin lambar na son jikinmu a duk lokuta... don samun ƙwarin gwiwa... daidai ne idan kika yi hakan kuma ko da ba ki yi ba ma ba komai.
''Bai kamata ki dinga jin kamar kin gaza ba a rayuwa, don kawai ba ki gamsu da tsarin jikinki ba a duk lokuta. Hakan daidai.
Erynn ta ce za ta ji daga bakin mutane ne kawai kan tunani biyu.
''Ko yaushe abu biyu na ke ji, ko dai 'Na tsani jikina... Ina son sauya wani sashe na jikina' ko kuma 'Ina son jikina, 'Ina da kyau, 'Na haɗu' wasu lokutan kuma na kan ji wasu sun ce 'Ni dai ba na son tsanar jikina' amma kuma ina ga bai min sosai yadda nake so ba.''
A ganinta, gano fafutukar alfahari da halittar ainihi ji take kamar an ɗauke mata wani babban nauyi.
Ta fara gano hakan ne a shafin sada zumunta na Tumblr ta kuma ce kwanan nan ta gano cewa bai kamata ta dinga jin hakan ba.
Kuma ba ita kaɗai ba ce.
Bidiyon da Erynn ta wallafa a shafinta na TikoTok @rynnstar ya ja hankalin mutane sosai inda zuwa yanzu aka so shi sau 52,000.
Fafutukar ta yi suna sosai, inda maudu'in #BodyNeutrality da ake amfani da shi aka kalle shi fiye da sau miliyan shida a TikTok da kuma sakamako fiye da 63,000 a shafin Instagram.
Amma yana kuma samun goyon baya.
Amma hakan na samun goyon bayan ƙwararu a harkar lafiyar ƙwaƙwalwa, inda ake amfani da wasu dabaru don taimakon mutanen da ke fama da jin cewa tsarin halittarsu bai musu ba.

Ta yaya zan bi wannan tsari kuma me ƙwararru suka ba da shawara a kai?
A cewar Erynn, za ki iya gwadawa kuma mafi kyan hanyar yin hakan ita ce ka dinga yi wa kanka magana.
''Idan kina kallon kanki a madubi, ba lallai ki iya cewa 'Ina da kyau' ba saboda wataƙila ba za ki iya cewa, 'Ni ƴar adam ce' don hakan yana da wuya gaskiya.
''Idan kina son cewa, 'Ni kyakyawa ce' to kawai ƴar budurwa ki faɗi hakan. Amma kuma idan kin ga za ki iya daure wa ki ce kawai, 'Ni mutum ce,; to faɗi abinki.''
Dr Morgan Francis, wata ƙwararriya kan lafiyar ƙwaƙwalwar jama'a tana koya wa mutanen da take duba wa yadda za su saba da ''alfahari da jikinsu'' wanda take jin wani bangare ne na ''gamsuwa da tsarin halittar da aka yi maka.''
''Duk abin ya ta'allaƙa ne kan me jikina zai taimaka min na yi... don girmama taimakon da jikinmu yake mana,'' a cewarta.
''Komai ya ta'allaƙa ne kan aikin da gaɓɓan jikinmu ke mana; yadda ƙafafunki ke sa ki zama jaruma, yadda hannayenki ke taimaka miki wajen riƙe jaririnki ko rungume shi.''
Dr Francis ta kuma jaddada cewa tsarin halittar jiki na ainihi ba wai yana nufin yin watsi da lafiyarka ba ne.
''Kina son samun ƙarfi da goyon-baya da samun taimakon jikinki amma kuma ba shi ne kaɗai abin da kike tunani ba.''
To mene ne abin da Dr Francis take ganin shi ne ƙashin bayan fafutukar nan ta tsarin halittar jiki ta ainihi? A taƙaice ta ce, ''tsarin halittar jiki ta ainihin shi ne waje mafi aminci kuma wanda mutane suka fi yarda shi.''



























