'Al'umma ke bai wa ɓarayi sunayen waɗanda suke sacewa'

Asalin hoton, AFP
Ɗabi'ar satar mutane don kuɗin fansa ta sake dawowa musamman a arewa maso yammacin Najeriya, to amma a wannan karon bayanai sun nuna cewa a na haɗa baki da wasu miyagu cikin al'umma wurin sace 'yan uwansu, kamar yadda BBC ta jiyo cikin hirar da tayi wani mutumin da a ka taba sacewa.
Lamarin sacewa tare da yin garkuwa da mutane ba sabon abu ba ne a yankin na arewa maso yammacin Najeriyar, musamman jihohin Kaduna da Katsina da Zamfara.
To amma wani abu sabo da a ka gano shi ne wasu mutanen na kwarmatawa ɓarayi bayanai game da mutanen da ke da hali, ko kuma waɗanda suka sayar da wata kaɗararsu,ko ma waɗanda su ka dawo daga balaguro ake tsammanin suna da kuɗi tare da su domin a sace su.
Ɗaruruwan irin waɗannan mutanen da ake sacewa sun rasa rayukansu, wasu da dama kuma sun yi asarar miliyoyin kuɗi ta hanyar biyan kuɗin fansa don ceton 'yan uwansu.
Hakan ya jefa da dama cikin talauci da kunci, yayin da daruruwa kuma suka tsallake rijiya da baya.
Wani mutun da aka sace amma aka sako a wata jihar da ke arewa maso yammacin kasar da dalilan tsaro ba za su bari mu bayyana sunansa ba ya yi bayanin yadda ya tsinci kansa a hannun masu garkuwa da mutane.
Ya fada wa BBC cewa ya shafe fiye da wata guda a hannun masu garkuwar, inda suka bukaci ya ba su milyoyin kudi kafin su sake shi.
''Sun kama mu ni da 'dan uwana su ka rufe mana ido su ka rika dukanmu wai don kar mu gudu.Ba sa bamu ruwa kuma abincin da su ke bamu bama iya ci''.
Sai dai yace daga karshe sun dai-dai ta ta waya da 'yan uwansa wadanda suka biya sama da naira miliyan daya a ka sako shi.
To amma ya tabbatar da cewa sun kashe ɗan uwansa saboda kasa biyan kudin da suka bukata.
''Daga karshe an kai musu naira miliyan ɗaya da dubu dari biyu, amma suka ce basu kai abinda su ke bukata ba, don haka su ka kaimu wani tsauni su ka riƙa dukanmu, daga baya ma sai su ka kashe ɗan uwana saboda ba a biya masa kudin fansa ba.''Ni kuma sai da a ka cika musu kuɗin kafin su ka sake ni.''
To amma ya ce masu garkuwar sun faɗa musu cewa suna da masu sanar da su waɗanda za su kama su samu kudi sosai, sai dai yace idan tsautsayi ya fadawa mutum suka kamashi a hanya to suna iya yi masa sassauci kasancewar basu san ko shi waye ba.
''Suna da mutanen da suke kira 'ƴan target' wadanda suke biya idan suka basu bayani game da mutun kuma suka yi nasarar garkuwa da shi.Suna da miyagun mutanen da ke ba su sirrin al'ummar da suke zaune tare da su.''
Musa Salmanu mai sharhi ne kan al'amuran taro a Najeriya yace tun da farko hukumomi sun yi sake matsalar ta girma kuma ya kamata gwamnati ta tashi tsaye tun kafin lamarin ya kara muni.
''Dole ne hukuma ta fito ta nuna karfinta ya zama ba sani ba sabo.A rika hukunta masu garkuwa da mutane da zarar an kama su don buga misali.''
Matsalar 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa ta zama wani kadagaren bakin tulu, duk da irin tabbaci da hukumomi suka sha bayarwa na shawo kan matsalar a sassan Najeriya lamarin da ya sa matafiya da mazauna gida ke zaune cikin fargaba da zulumi saboda rashin tabbas, musamman a jihohin arewa maso yamma.



























