Hotunan mako na Afirka daga 18 zuwa 24 ga watan Satumban 2020

An wallafa

Wasu zaɓaɓɓun hotuna masu ƙayatarwa na wannan makon a Afirka:

Wata mata na ƙwasar shara a Hout Bay shoreline na Cape Town, Afirka ta Kudu, yayin da duniya tayi bikin ranar tsafta ta duniya ranar Asabar
Bayanan hoto, Wata mata na kwasar shara a gabar tekun Hout Bay na Cape Town, Afirka ta Kudu, yayin da duniya ta yi bikin ranar tsafta ta duniya ranar Asabar
A ranar Lahadi, mambobin ƙungiyar Al-Nour Wal Amal ta mata makafi na kida a wasan su na farko bayan dakatar da komai na tsawon watanni saboda annobar korona a fadar Manaterly da ki birnin Alkhahira na Masar
Bayanan hoto, A ranar Lahadi, mambobin ƙungiyar Al-Nour Wal Amal ta mata makafi na buga goge a wasansu na farko bayan dakatar da komai na tsawon watanni saboda annobar korona a fadar Manaterly da ke birnin Alkhahira na Masar
Goggon biri na shayar da yan biyun da ta haifa a gidan namun daji Virunga da ke Jamhuriyar Demokradiyar Congo ranar Talata
Bayanan hoto, Goggon biri na shayar da yan biyun da ta haifa a gidan namun daji Virunga da ke Jamhuriyar Demokradiyar Congo ranar Talata
Washe gari an iske yadda wani jami'in tsaro ke rike da kare sun kewaye tittunan birnin Accra gabanin zabukan da ke tafe a watan Disamba
Bayanan hoto, Washegari an ga wani jami'in tsaro rike da kare suna kewaye titunan birnin Accra gabanin zabukan da ke tafe a watan Disamba
A ranar Lahadi, mai fafutika ƴar Somalia Fatuna Musa Afrah cikin masu zanga-zanga da aka shirya a Berlin na Jamus, ta na neman ƴancin baki ƴan gudun hijira daga Girka da kwashe su daga sasanonin da aka kebe su
Bayanan hoto, A ranar Lahadi, mai fafutuka ƴar Somalia Fatuna Musa Afrah cikin masu zanga-zanga da aka shirya a Berlin na Jamus, tana neman ƴancin baki ƴan gudun hijira daga Girka da kwashe su daga sasanonin da aka kebe su
Bayan kwana biyu, Ƴan Mali sun yi amfani da bikin cika shekara 60 da samun ƴancin kai wajen gangamin adawa da cigaba da kasancwar dakarun Faransa a Kasar.
Bayanan hoto, Bayan kwana biyu, Ƴan Mali sun yi amfani da bikin cika shekara 60 da samun ƴancin kai wajen gangamin adawa da ci gaba da kasancewar dakarun Faransa a Kasar.
A ranar Juma'a mutane daga birnin Rabat na Moroko sun kona tutar Isra'ila a wata zanga-zangar nuna rashin gamsuwa da daidaita alaka tsakanin kasashen biyu.
Bayanan hoto, A ranar Juma'a mutane daga birnin Rabat na Moroko sun kona tutar Isra'ila a wata zanga-zangar nuna rashin gamsuwa da daidaita alaƙa tsakanin ƙasashen biyu.
Mazan Maasai na Matapato sun halarci bikin Olng'esherr na cin nama da ake gudanarwa a dutsen Maparasha na Kajiado a Kenya ranar Laraba...
Bayanan hoto, Mazan Maasai na Matapato sun halarci bikin Olng'esherr na cin nama da ake gudanarwa a dutsen Maparasha na Kajiado a Kenya ranar Laraba...
...bayan dage bikin sakamakon annobar korona. Bikin na hada kawunan tsoffi Ilpaamu da matasan Ilaitete su kasance abokan juna
Bayanan hoto, ...bayan dage bikin sakamakon annobar korona. Bikin na haɗa kawunan tsoffi Ilpaamu da matasan Ilaitete su kasance abokan juna
Kwamitin Sufi na taro da kade-kade da wakokin addini domin tunawa da Sidi Omar Boukhtiwa a birnin Tunis na Tunisia ranar Lahadi
Bayanan hoto, Kwamitin Sufi na taro da kaɗe-kaɗe da wakokin addini domin tunawa da Sidi Omar Boukhtiwa a birnin Tunis na Tunisia ranar Lahadi
A ranar Juma'a masu kera akwatin gawa a Harare na Zimbabwe na kammala aikin kera wani akwaitin gawa
Bayanan hoto, A ranar Juma'a masu sassaƙa akwatin gawa a Harare na Zimbabwe na kammala aikin ƙera wani akwatin gawa
Dean Burmester na Afirka ta Kudu na duba rami na 6 da kwallon gulf ya fada, a rana ta farko na gasar Irish Open ranar Alhamis
Bayanan hoto, Dean Burmester na Afirka ta Kudu na duba rami na 6 da ƙwallon gulf ya faɗa, a rana ta farko na gasar Irish Open ranar Alhamis

Hotuna daga Reuters, PA and EPA.