Time 2020: Tony Elumelu, Tomi Adeyemi da Tunji Funsho sun shiga jerin masu ƙarfin faɗa a ji a duniya

Tony Elumelu and Tomi Adeyemi
Bayanan hoto, Tony Elumelu da marubuciya Tomi Adeyemi su ne ƴan Najeriyar da ke cikin jerin sunayen masu faɗa aji a duniya.
An wallafa

Mujallar Time ta saki jerin sunayen mutum 100 da ta ce masu ƙarfin faɗa a ji a duniya a 2020.

Sunayen sun ƙunshi shugabannin ƙasashen duniya da ƴan kasuwa da fitattun mutane a fannin fina-fina da wasanni.

Bana an shiga yanayi na annobar korona wacce ta tilasta wa duniya zaman kulle.

Amma, daga cikin jerin sunayen, akwai ƴan Najeriya uku saboda tasirinsu ga tattalin arzikin Afrika, da fannin lafiya da fasaha.

Tony Elumelu

Tony Elumelu

Attajirin Afrika, Aliko Dangote na jinjina wa shugaban bankin UBA.

Dangote yana yaba wa aikin da yake tare da cibiyar Tony Elumelu domin taimaka wa matasa ƴan kasuwa wajen bunƙasar kasuwancinsu.

Shirin wanda aka fara a 2015, shi ne mafi girma a nahiyar Afirka.

Tunji Funsho
Bayanan hoto, Tunji Funsho ne ya taimaka wajen kawar da cutar foliyo a Najeriya.

Tunji Funsho

Editan Mujallar Time, Jeffery Kluger ya yi rubutu game da ƙwararren likitan zuciya kan girman aikinsa na kawar da cutar foliyo a Najeriya.

A ranar 25 ga Agustan 2020, aka tabbatar da cewa babu sauran cutar foliyo a Najeriya, kuma Dakta Funsho a 2018 ya ce babban burinsa shi ne tabbatar da babu wani yaro a Najeriya da yake fama da cutar.

Mista Kluger ya ce, "Dakta Funsho ya yi ƙokarin ganin an kawo ƙarshen cutar a ƙasar, ta hanyar haɗin guiwa da gidauniyar Bill da Melinda Gates da WHO da CDC da kuma UNICEF domin samun rigakafi ga mutanen ƙauye da kuma bayar da tallafi wajen wayar da kan mutane."

Tomi Adeyemi

Tomi Adeyemi

Jarumi a Landan John Boyega, ya yi rubutu game da ita cewa "hikimominta za su samar da ayyukan yi fa da kuma samun wakilci ga masana'antar"

Tomi Adeyemi ita ta rubuta littafi mai taken "Children of Blood and Bone" wanda aka bayyana kamar irin na Harry Potter, tarihin Narnia da kuma gumakan Yarabawa.

Littafin ya samu lambar yabo ta marubuta ƴan Najeriya, Amurkawa a 2019 kuma ya yi fice har Disney/Fox a 2019 ya ce zai mallake shi.