Auren Sadiya Farouk, Gobarar tankar mai a lokoja, da kisan Kanar Bako

An wallafa

Zaben Edo: INEC ta ce Gwamna Obaseki na PDP ya doke Ize-Iyamu na APC

..

A farkon makon da ya gabata ne ranar Lahadi kenan hukumar INEC a Najeriya ta sake tabbatar da Godwin Obaseki na Jam'iyyar PDP a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Edo a karo na biyu, bayan ya doke abokin hamayyarsa na Jam'iyyar APC, Fasto Osagie Ize-Iyamu.

Wannan ne karo na biyu da Obaseki ke doke Ize-Iyamu, inda a 2016 ma hakan ya faru, amma lokacin Obaseki na APC, Ize-Iyamu kuma a PDP.

Hukumar ta INEC ta bayyana cewa Mista Obaseki ya samu ƙuri'u 307, 955 inda kuma Mista Osagie Ize-Iyamu ya samu ƙuri'u 223,619.

Ɗan takarar Jam'iyyar SDP ne ya zo na uku da ƙuri'u 323, sai kuma na Jam'iyyar LP da ya samu ƙuri'u 267.

Sarkin Zazzau Shehu Idris ya rasu

..

A ranar Lahadin ne dai Allah Ya yi wa Sarkin Zazzau, Dakta Shehu Idris rasuwa, inda aka yi jana'izarsa da yammacin ranar.

Rahotanni sun ce Sarkin ya rasu ne bayan gajeruwar jinya ta mako biyu a wani asibiti da ke Kaduna.

Marigayi Shehu Idris ya rasu yana da shekara 84, bayan shafe shekara 45 kan karagar mulki a Masarautar Zazzau.

Manyan mutane da da dama da suka haɗa sarakuna da gwamnoni da ministoci da manyan ma'aikatan gwamnati sun je birnin na Zaria domin yin ta'aziyya bisa rasuwar sarkin.

Kanar DC Bako: 'Yan Najeriya sun fusata kan kisan da Boko Haram ta yi wa Kwamandan sojin ƙasar

..

A ranar Litinin ne rundunar sojin Najeriya ta bakin rundunar Lafiya Dole, ta tabbatar da mutuwar Kanar DC Bako, wanda ta ce ya mutu sakamakon raunuka da ya samu bayan kwanton-ɓaunan da mayaƙan Boko Haram suka yi wa tawagarsa a yankin Sabon Gari-Wajiroko kusa da Damboa jihar Borno ranar Lahadi.

Dakarun da yake jagoranta sun ragargaji mayaƙan da suka yi musu kwanton-ɓauna inda suka kashe 'yan ta'adda da dama sannan suka ƙwato makamai da na'urori, a cewar sanarwar da mai magana da Runduna Ta Bakwai Ado Isa ya fitar.

"Abin baƙin ciki shi ne an raunata shi a lokacin da yake ɓa-ta-kashi kuma nan take sojin sama na rundunar Lafiya Dole suka ɗauke shi zuwa asibitin Runduna ta Bakwai 7 da ke Maimalari. Marigayi babban jami'in rundunar sojin yana cike da kazar-kazar kuma ya yi sallar Asuba da safiyar yau kafin mutuwarsa a asibitin," a cewarsa.

Kisan da aka yi wa babban sojan ya tayar da hankalin 'Yan Najeriya da dama inda suka yi ta sukar tsarin tsaron Najeriya.

Auren Sadiya Farouk da shugaban sojojin sama na Najeriya

..

A makon da ya gabata ne BBC ta tabbatar da an ɗaura auren Ministar Jin-ƙai da kare Afkuwar Bala'i ta gwamnatin Najeriya Hajiya Sadiya Farouq da shugaban rundunar sojin saman ƙasar Sadiq Baba Abubakar, bayan tuntuɓar wasu makusantan mutanen biyu.

Majiyoyin masu ƙarfi ta ɓangaren Minista Sadiya da Air Marshal Sadiq da suka buƙaci a ɓoye sunayensu sun ce an ɗaura auren ne cikin sirri a Abuja babban birnin ƙasar.

Sai dai daga Ministar har shugaban rundunar sojin saman ba su fito sun gaskata ko ƙaryata batun ba har yanzu.

Sai dai ƴan Najeriya da dama na mamakin yadda za a ɗaura auren fitattun mutane irin waɗannan amma ba a bayyana lamarin ba, musamman ganin cewa aure abin alkhairi ne ba abin ɓoyewa ba.

Gobara a Lokoja: Bindigar tankar mai ta yi sanadin mutuwar mutane da dama

..

A ranar Larabar da ta gabata ne hukumomi a jihar Kogi suka ce aƙalla mutum 28 suka rasa rayukansu a wani haɗarin tankar mai da ya faru a garin Lokoja na jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya.

Ganau dai sun ce lamarin ya faru da safiyar yau Laraba, lokacin da wata tankar mai ta ƙwace daga mai tuƙinta ta afka kan ababen hawa da ke tafiya, lamarin da ya yi sanadiyyar kifewarta kuma ta kama ta wuta.

Wani mazaunin garin wanda ya je wurin bayan afkuwar haɗarin direban motar, ya yi ƙoƙarin sanar da mutane su kauce amma ba a kula shi ba.

Lamarin ya faru ne a yankin Felele kuma hotunan da aka watsa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda mutane da dama suka ƙone ƙurmus.