An saki yaran da aka tsare a Masar saboda shiga zanga- zanga

Masu gabatar da kara a Masar sun saki fiye da kananan yara 70 da aka tsare yayin zanga-zangar kin jinin gwamnati.
An sake su ne bayan da iyayensu suka yi alkawarin hana su shiga duk wata hatsaniya a nan gaba.
A baya bayan nan an samu rahotannin lalata kayayyakin gwamnati yayin zanga - zanga a wasu garuruwa.
Masu zanga - zangar na nuna fushinsu ne dangane da yadda gwamnati ke yin gine - gine a duk in da taga dama ba tare da sanar da jama'a ko kuma biyansu diyya ba.
A Masar dai doka ta haramta duk wata zanga-zanga, abin da ke janyowa shugabannin kasar suka daga kungiyoyin 'yan gwagwarmaya na duniya.
Karuwar take hakki karkashin mulkin Al-Sisi

Asalin hoton, Getty Images
A shekarar 2013 ne, Abdel Fattah al-Sisi, ya jagoranci sojin Masar suka hambarar da gwamnatin shugaba na farko da aka zaba a tsarin dimukradiyya marigayi Muhammad Morsi, bayan zanga-zangar kin mulkinsa.
Tun daga lokacin kungiyoyin kare hakkin dan adam ke zargin gwamnati da take hakkin jama'a, da kame dubban 'yan adawa ciki har da tsare marigayi Morsi wanda a shekarar nan ya rasu a kotu a ranar da ake zaman sauraron karar da ake masa.
Sai dai shugaba Abdel Fattah al-Sisi, ya musanta zargen-zargen inda ya kira su na karya tsagwaronta.
Majalisar dokokin Masar ta kada kuri'ar amincewa da daftarin sauye-sauyen tsarin mulki da ka iya tsawaita lokacin Shugaba Abdul Fattah al-Sisi kan karagar mulki da wasu shekaru 12.
Mista Sisi zai sauka a 2022 lokacin da wa'adinsa na biyu na shekaru hudu ya kare.



























