Abubuwan da suka faru a Najeriya a makon jiya

An wallafa

Ga wasu daga cikin abubuwan da suka faru a makon da ya gabata tun daga Lahadi, 4 ga watan Oktoban 2020 zuwa Asabar, 10 ga wata.

Matar da ake zargi ta kashe ƴaƴanta a Kano 'tana da aljanu'

Kano Police PPRO KANO POLICE PP

Mahaifiyar matar da ake zargi ta kashe ƴaƴanta guda biyu a jihar Kano da ke Najeriya ta ce 'yarta ta daɗe tana rashin lafiyar da ke da nasaba da iskokai.

A ranar Asabar ne rundunar 'yan sandan Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wasu yara biyu mace da namiji yan shekara uku da kuma shida da ake zargin mahaifiyarsu ce ta kashe su.

Lamarin wanda ya faru a Unguwar Sagagi Layin 'Yan Rariya a birnin Kano, da farko an bayyana cewa sabani ne da mijinta saboda ya yi mata kishiya a watannin baya ya kai ga kisan ƴaƴansu.

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce jami'anta sun kama matar yanzu haka tana hannunsu, kuma ta tabbatar da cewa ita ta kashe ƴaƴanta, kamar yadda kakakin rundunar ya shaida wa BBC.

An naɗa sabon sarkin Zazzau

ZAZZAU EMIRATES/FACEBOOK
Bayanan hoto, Sabon Sarkin Zazzau Ahmad Nuhu Bamalli

A ranar Laraba ne gwamnan jihar Kaduna ya naɗa Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin Sabon Sarkin Zazzau.

Ya maye gurbin Mai Martaba Alhaji (Dr.) Shehu Idris wanda ya rasu ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba 2020, bayan ya kwashe shekara 45 yana kan mulki."

Tun a ranar Laraban ne sabon sarkin ya shiga Fadar ta Zazzau, sa'o'i kaɗan bayan sanar da ba shi sarautar.

Alhaji Bamalli shi ne sarki na farko daga gidan Mallawa cikin shekara 100 da suka gabata, bayan rasuwar kakansa Sarki Dan Sidi a shekarar 1920.

Kasafin Kuɗin Najeriya na 2021: Buhari ya gabatar wa majalisa kasafin naira tiriliyan 13.08

Nigeria Presidency
Bayanan hoto, Shugaba Buhari na najeriya a majalisar kasar

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kuɗin ƙasar kimanin naira tiriliyan 13.08 na shekarar 2021 a gaban Majalisar Dokokin ƙasar - a zaman hadin gwiwa tsakanin majalisar dattawa da ta wakilai.

Hasashen kuɗin ya fi na bara da tiriliyan 2.28, inda na baran ya kasance naira tiriliyan 10.805.

A yayin da yake gabatar da kuɗin Shugaba Buhari ya ce samun kuɗaɗen shiga don amfani da su wajen kasafin kuɗin shi ne babbar matsalar da gwamnatinsa ke cin karo da shi.

Sannan kuma ya ce ministoci za su dinga sa ido don tabatar da cewa hukumomin karɓar kuɗaɗen haraji na ayyukansu yadda ya kamata.

'Yadda ƴan bindiga suka yi wa mata shida fyaɗe a gabana'

BBC

Musa Adamu da ke zaune a ƙauyen Mallamawa ya tsere daga hannun ƴan fashin da suka sace shi bayan ya shafe kwana biyu a jihar Katsina da ke a arewa maso yammacin Najeriya.

Mutumin wanda ke da ƴaƴa 10 da matan aure biyu, ya shaida wa BBC cewa ƴan bindiga kusan 50 ne suka shiga gonarsu a ranar Lahadi da safe, inda suka kama shi tare da abokinsa da wasu mutanen da ke wasu gonakin na kusa da nasu.

"Ina cikin gonata ina girbe gero tare da abokina sai ga mutanen sun shigo a kan babura ɗauke da bindigogi, kafin mu yi wani abu har sun tattara mu sun ɗora mu a kan baburan.

''Daga nan suka kuma shiga sauran gonakin suka sace wasu mutanen suka haɗa mu duka. Kusan mu 12 suka ɗauke a ƙauyan Mallamawa," in ji shi.

''A cikinmu akwai mata huɗu, uku ƴan mata sai matar aure ɗaya, inda suka dinga bin su da ɗai-ɗai suna musu fyaɗe a gabanmu.

'Yan Najeriya na zanga-zangar kawo ƙarshen SARS

EPA

Ƴan Najeriya musamman ƴan kudancin ƙasar sun jima suna ta kiraye-kiraye kan soke rundunar da ke yaƙi da fashi da makami ta SARS.

Sun kuma sha yin zanga-zangar lumana kan tituna, a wani lokacin kuma a kafafen sada zumunta inda suke amfani da mau'du'in #ENDSARS.

Suna gudanar da zanga-zangar ne sakamakon zargin da suke yi wa rundunar ta SARS da azabtarwa da kisa ba bisa ƙa'ida ba da kuma saɓa ƙa'idojin aiki.

Sai dai a wannan karon, da alamu haƙarsu ta soma cimma ruwa sakamakon dagewa da suka yi kan wannan zanga-zanga, lamarin da har ya ja hankalin shugaban ƙasar ya fito ya ce zai ɗauki matakin kawo sauyi a rundunar.