NoBraDay: Alamun cutar kansar mama da hanyoyin kare kanki

Mata na kallon waya
An wallafa

Kansar mama ita ce cutar daji da mata suka fi fama da ita inda take shafar aƙalla mace miliyan biyu da dubu ɗari ɗaya duk shekara, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya WHO.

An ware watan Okotoban kowace shekara a matsayin watan wayar da kai kan cutar sankarar mama a faɗin duniya.

Hakan ne ma ya sa a ranar Talata 13 ga watan Oktoba aka wayi gari da maudu'in #NoBraDay yana tashe a shafukan sada zumunta da muhawara na Najeriya.

WHO ta kuma ce cutar kansar mama ita ce cutar da ta fi janyo mace-macen da suka danganci cutar daji a mata.

Amma hukumar ta ce idan aka gano ta da wuri, ana iya warkewa daga cutar ta sankarar mama. Shi ya sa ma ake yawan bai wa mata shawarar yin gwaji akai akai.

Sai dai abin tashin hankalin shi ne idan ba a shawo kan cutar da wuri ba tana iya sanadin da za a yanke wa mace mamanta don samun sauƙi.

Alamun kansar mama

  • Babbar alama ta kansar mama ita ce ɓullar ƙurji a jikin maman wanda a da babu shi
  • Idan girman maman ya sauya ta hanyar raguwa ko ƙaruwa, ga mama ɗaya ko duka biyun
  • Idan wani ruwa yana fita daga kan maman
  • Idan kaluluwa ta fito ƙasan hammatar mace
  • Idan wani ɓangare na maman ya ɗan loɓa ciki
  • Idan aka ga wasu ƙuraje sun fito a kan maman
  • Idan kika ga wani sauyi kan nonon, ko kuma kan nonon ya fara lumewa ciki.
  • Sai dai masana lafiya sun ce ba kowane ciwon nono ne yake zama alamar kansar mama ba.
Wannan layi ne

Baya ga wannan, ga wasu abubuwa da WHO ta ce idan aka bi ƙa'idarsu ana iya gujewa kamuwa da sankarar mama.

Mace ta tallafi mamanta

1. Daina shan taba sigari.

A fadin duniya, taba sigari ita ce ɗabi'a ɗaya tilo da idan aka guje mata ake iya kaucewa shiga haɗarin kamuwa da cutar daji. Tana kashe a kalla mutum miliyan 6 duk shekara.

Taba sigari na da sinadarai masu haɗari sama da 7000 kuma fiye da guda 50 daga cikinsu na janyo cutar sankara ta ko wane ɓangare na jiki.

Shanta na janyo cutar daji a huhu da ciki da makogwaro da mama da koda da hanta da sauransu.

2. Cin abinci mai gina jiki da yawan motsa jiki na bayar da kariya daga cutar daji.

Bincike ya nuna cewa mata masu ƙiba sun fi haɗarin kamuwa da sankarar mama. Amma cin abinci mai dauke da kayan lambu da kayan marmari na gyara garkuwar jiki da inganta yadda jiki ke sarrafa sinadaransa.

Yawan motsa jiki da tabbatar da cewa ba a saki teɓa ba na rage haɗarin kamuwa da cutar dajin.

3. Shan barasa na cikin abubuwan da ke jefa mata cikin haɗarin kamuwa da cutar sankarar mama.

Wani bincike da aka gudanar a 2010, WHO ta ce a kalla shan barasa na janyo mutuwar mutane 337,400 ta hanyar cutar daji a faɗin duniya.

4. Gurbacewar muhalli na daga cikin abubuwan da ke haifar da cutar daji.

Gurbatacciyar iska da gurbataccen ruwa da gurbatacciyar ƙasar noma na kara jefa mutane cikin haɗarin kamuwa da sankara.

WHO ta yi kiyasin cewa gurbatacciyar iska na janyo mutuwar aƙalla mutum miliyan uku da dubu ɗari biyu.

Ƙarin labarai masu alaƙa