Waiwaye: Sheikh Dahiru Bauchi ya gana da Buhari, za a rusa NNPC
Wannan maƙala ta zaƙulo labaran abubuwan da suka faru ne a makon da muke ban kwana da shi.
Rushe kamfanin NNPC

Asalin hoton, State House
Fadar shugaban Najeriya ta tabbatar da cewa za a rusa babban kamfanin na kasar NNPC a cikin sauye-sauyen da za a iya wa fannin man kasar karkashin sabuwar dokar inganta harkokin man fetur.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya tabbatar da hakan a tattaunawarsa da BBC.
Sai dai ya ce za a maye gurbinsa da wani kamfanin mai zaman kansa.
Wannan na daga cikin ayukkan da aka dorawa kwamitin share fage kan aiwatar da dokar da Shugaban Muhammadu Buhari ya sanar da kafawa a dazu yayin taron majalisar ministoci na mako-mako.
Ɗage shari'ar Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara

Kotu a jihar Kano da ake arewa maso yammacin Najeriya ta ɗage sauraron ƙarar Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara zuwa 2 ga Satumban 2021.
A ranar Laraba ne Alkali Ibrahim Sarki Yola ya ɗage sauraron ƙarar bayan da aka yi zama na biyu tun fara shari'ar a birnin Kano.
Gwamnatin jihar Kano ce ta shigar da ƙarar Malam Abduljabbar kan zarginsa da yin kalaman ɓatanci ga Annabi SAW.
Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce sosai a faɗin ƙasar ba ma jihar Kano kaɗai ba.
Wakilinmu na Kano Khalifa Shehu Dokaji ya ce ya ga Abduljabbar Kabara ya rame a wannan zaman kotu na biyun da aka yi ranar Laraba.
Mai Shari'a Sarki Yola ya ce ya ɗage sauraron ƙarar ne saboda duk hujjojin da aka gabatar sun yi masa tsauri ya yanke hukunci nan take.
Ganawar Buhari da Dahiru Bauchi

Asalin hoton, Buhari Sallau
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin Sheik Dahiru Bauchi a fadarsa da ke Abuja.
A ranar Laraba ne babban malamain ya kai wa shugaban ziyarar sai dai babu wani rahoto da ke bayyana abin da suka tattaauna ya zuwa yanzu.
Duk da cewa babu tartibin abin da suka tattauna, amma rahotanni na cewa hakan ba ya rasa alaka da kisan da aka yi wa wasu matafiya a makon da ya wuce a jihar Plateau da ke arewacin Najeriya.
Kimanin mutum talatin ne suka mutu sakamakon wani hari da ake zargin `yan kabilar Irigwe da kaiwa kan motar matafiyan a cikin birnin Jos, amma sun musanta wannan zargi.
Sake nada shugaban NUC da na JAMB

Asalin hoton, Presidency
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tabbatar da sake naɗin shugaban JAMB Farfesa Ishaq Olanrewaju Oloyede da Shugaban hukumar Jami'o'i Farfesa Abubakar Adamu Rasheed.
Wannan ya biyo bayan shawarar da ministan Ilimi na kasar ya ba shi Adamu Adamu.
An nada su ne duka na tsawon shekaru biyar, wanda hakan zai fara aiki daga 1 ga watan Agusta 2021.
Haka kuma ya sake naɗa Dr Hamid Bobboyi shugaban hukumar ilimin bai daya a karo na biyu na tsawon shekaru hudu masu zuwa shima zai fara aiki a ranar 1 ga watan.
Mutum 50 da suka mutu saboda kwalara a Sokoto

Cutar Kwalara ta kashe mutum 50 a jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya.
Kwamishinan lafiya na jihar Dr Muhammad Ali Inname ya bayyana wa manema labarai hakan a yayin taron kwamitin koli na jihar, inda ya ce jihar Sokoto na daukar matakan gaggawa da suka dace kan matsalar.
Yace kananan hukumomi 22 cikin 23 an samu bullar cutar a cikinsu, ya kara da cewa kuma ana tsammanin cutar ta bulla ne daga cikin shara da ake zubarwa a ko ina, da yadda ake bayan gari a ko ina, da rashin tsafta da dai sauran abubuwa da yawa.
Dr Ali ya kara da cewa, gwamnati na samun rahoton cutar ta tayar da wata tawaga ta musamman domin kai dauki kananan hukumomin da cutar ta bulla.
Kwararar miyagun kwayoyi da aka samu a Jihar Bauchi

Asalin hoton, NDLEA
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce an samu kwararar hodar iblis da sauran miyagun kwayoyi a Jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya.
Kwamandan da ke lura da jihar , Segun Oke ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a jihar, yayin kaddamar da wata tawaga da za ta yi yaki da amfani da miyagun kwayoyi, inda ta ce ta gano wurare masu yawa da ake sayar da hodar iblis din kuma ake safararsu.
"Har yanzu muna bincike kan wadanda suke fasakaurinta zuwa wannan jihar" in ji Oke.
Shugaban ya ce an kama mutane da yawa yayin kamen da aka yi a Bauchi.
Umarnin gwamnatin Katsina na mutane su dauki makamai don kare kansu

Asalin hoton, KTGS
Gwamnan Jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ya buƙaci mazauna garuruwan da 'yan bindiga ke yawan kai wa hare-hare da su nemi makamai don kare kan su daga hare-haren.
Aminu Bello Masari ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin da ya kai ziyarar jaje a Ƙaramar Hukumar Jibia ga iyalan mutum 10 da jami'an hukumar kwastan suka kashe a makon da ya gabata.
Katsina na cikin jihohin da 'yan bindiga suka fi kashewa tare da yin garkuwa da mutane a arewa maso yamnmacin Najeriya.
Ranar 11 ga watan Disamba 'yan bindigar da ake zargin 'yan fashin daji ne suka sace ɗalibai daga sakandaren garin Kankara na jihar ta Katsina guda 344, inda suka shafe kwana shida a hannun masu garkuwar.
Daurin auren Yusuf Buhari da Zarah Bayero

Asalin hoton, WRAITH STUDIOS
An ɗaura auren Yusuf Muhammadu Buhari da Zahra Nasir Bayero a garin Bichi kan sadaki naira 500,000.
Aminu Dantata ne waliyyin amarya yayin da Malam Mamman Daura ne waliyyin ango. Ministan Sadarwa Malam Isa Ali Pantami ne ya daura auren na Yusuf da Zahra.
An ɗaura auren ne da misalin ƙarfe 2:38 na ranar Juma'a.
Manyan jami'an gwamnati da ƴan siyasa da suka haɗa da gwamnoni da ƴan majalisa da ministoci da dai saurensu.
An tsaurara tsaro a gidan Sarkin Bichi da kuma masallacin Bichi, inda a nan ne aka daura auren Yusuf, ɗan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Zahra, ƴar Sarkin Bichi Nasiru Ado Bayero.
Haka kuma akwai jami'an tsaro a duka titunan cikin garin.



























