Kasuwar 'Yan kwallo: Maomar Mbappe, Ronaldo, Arteta, Kane, Guardiola, Loftus-Cheek

Kylian Mbappe
Bayanan hoto, Tun da farko Real Madrid ta taya Mbappe yuro miliyan 160
An wallafa

Paris St-Germain na son Real Madrid ta lale mata yuro miliyan 220 (fam miliyan 188) idan har tana son dan gabanta na Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 22. (Jaridar Le Parisien)

Manchester City ba ta kawar da yuwuwar sayen dan gaban Juventus da Portugal ba Cristiano Ronaldo, mai shekara 36, bayan da kyaftin din Ingila Harry Kane ya tabbatar da ci gaba da zamansa a Tottenham. (Jaridar ESPN)

Cristiano Ronaldo

Kane ya damu ganin yadda shugaban Tottenham Daniel Levy bai zai yarda a sayar da shi ba, wanda hakan ya sa dan wasan mai shekara 28, zai kulla sabuwar yarjejeniya wadda za ta kunshi damar barinsa ya tafi. (Telegraph)

Pep Guardiola zai bar Manchester City idan kwantiraginsa ya kare bayan kakar 2022-23, sannan ya dauki hutu daga harkar kwallon kafa, kafin daga bisani ya karbi aikin horad da tawagar kasa. (Globo, daga Manchester Evening News)

Kociyan Arsenal Mikel Arteta ba ya cikin hadarin rasa aikinsa, duk da yadda kungiyar ta fara gasar Premier da rashin sa'a. An rika yada cewa tsohon kociyan Chelsea Antonio Conte ne zai maye gurbinsa. (Independent)

Mikel Arteta na san suka saboda fara gasar Premier da rashin sa'a
Bayanan hoto, Mikel Arteta na san suka saboda fara gasar Premier da rashin sa'a

Kociyan Roma Jose Mourinho na shirin taya dan wasan tsakiya na Chelsea, dan Ingila Ruben Loftus-Cheek fam miliyan 13 da rabi. Dan wasan mai shekara 25 ya yi aiki na dan lokaci da Mourinho a karo na biyu da kociyan ya horad da Blues. (Mail)

Manchester United ba za ta iya taya ko dai dan wasan tsakiya na Rennes, dan Faransa Eduardo Camavinga, mai shekara 18, ba ko kuma dan wasan tsakiya na Atletico Madrid dan Sifaniya Saul Niguez, mai shekara 26 ba, sai dai idan za ta sayar da wasu 'yan wasanta ta samu kudin cinikin. (ESPN)

Ana ganin Chelsea ce ke da dama sosai ta sayen Niguez, wanda Atletico ke son sayar da dan wasan na tawagar Sifaniya. (Express)

Niguez

Sevilla ta ce ta yi watsi da bukatar Chelsea ta sayen dan bayanta, dan Faransa Jules Kounde mai shekara 22, kuma ta ce ba ta da niyyar sayar da wani dan wasa. (Goal)

Kila Chelsea ko RB Leipzig dan wasan tsakiya na Barcelona Ilaix Moriba zai tafi, idan matashin dan wasan dan Guinea mai shekara 18ya ki sabunta kwantiraginsa da Barca. (Mundo Deportivo)

Dan wasan Arsenal, dan Brazil, Willian, mai shekara 33, na kokarin kulla yarjejeniyar tafiya Corinthians ta kasarsa. (Sun)

Willian

Dan wasan tsakiya na Barcelona da Sifaniya Sergio Busquets ya yarda a kara rage masa albashi kuma a biyan nasa zua wani lokaci, domin taimaka wa kungiyar rage nauyin da yake kanta na biyan albash. (ESPN)

Tsohon dan wasan tsakiya na Arsenal dan Ingila Jack Wilshere, mai shekara 29, ya ce yana tunanin yin ritaya kasancewar bai samu gayyata daga wata kungiya ba tun bayan da Bournemouth ta sallame shi. (Athletic)