Ƙayatattun hotunan Afrika na wannan makon: Daga 20-26 ga Agustan 2021

An wallafa

Wasu daga cikin zaɓaɓɓun hotunan ƴan Afrika daga nahiyar ta Afrika da kewaye.

A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne aka naɗa Yarima Tsola Emiko a matsayin sabon sarki na Warri da ke Najeriya, wato Olu na Warri
Bayanan hoto, A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne aka naɗa Yarima Tsola Emiko a matsayin sabon sarki na Warri da ke Najeriya, wato Olu na Warri
A Liberia, mutanen ƙasar ne suka fito domin murna da ranar tuta ta ƙasar wadda alama ce ta ranar samun ƴancin ƙasar daga Amurka.
Bayanan hoto, A Liberia, mutanen ƙasar ne suka fito domin murna da ranar tuta ta ƙasar wadda alama ce ta ranar samun ƴancin ƙasar daga Amurka.
A Libiya kuma, jama'a ne suka taru a Tripoli a ranar Juma'a domin cikar ƙasar shekara goma cif da ƙwace ikon birnin daga tsohon shugaban ƙasar Muammar Gaddafi
Bayanan hoto, A Libiya kuma, jama'a ne suka taru a Tripoli a ranar Juma'a domin cikar ƙasar shekara goma cif da ƙwace ikon birnin daga tsohon shugaban ƙasar Muammar Gaddafi
A nan kuma, Kiristoci ne ƴan ɗarikar Orthodox ke tasu murna da kuma bikin cika ciki a ranar Lahadi, kwanaki 15 bayan sun kammala azumi.
Bayanan hoto, A nan kuma, Kiristoci ne ƴan ɗarikar Orthodox ke tasu murna da kuma bikin cika-ciki a ranar Lahadi, kwanaki 15 bayan sun kammala azumi.
Wannan wata mata ce ke tsinkar ganyen shayi a Kenya - ƙasar ce ta uku a duniya wajen samar da baƙin shayi da kuma fitar da shi zuwa sauran ƙasashe.
Bayanan hoto, Wannan wata mata ce ke tsinkar ganyen shayi a Kenya - ƙasar ce ta uku a duniya wajen samar da baƙin shayi da kuma fitar da shi zuwa sauran ƙasashe.
Yadda ruwan sama mai ƙarfi kenan ya jawo ambaliyar ruwa a Senegal, lamarin da ya tilasta wa mutane da dama barin gidajensu a Dakar babban birnin ƙasar
Bayanan hoto, Yadda ruwan sama mai ƙarfi kenan ya jawo ambaliyar ruwa a Senegal, lamarin da ya tilasta wa mutane da dama barin gidajensu a Dakar babban birnin ƙasar
Dubban kaji ne suka sha wuƙa a Ivory Coast, ƙasar da ke fama da ɓarkewar wani nau'in murar tsuntsaye
Bayanan hoto, Dubban kaji ne suka sha wuƙa a Ivory Coast, ƙasar da ke fama da ɓarkewar wani nau'in murar tsuntsaye
A Afrika Ta Kudu kuwa, ana amfani da jirgin ƙasa ne wajen jigilar riga-kafin korona zuwa garuruwan da ababen hawa ke wahalar shiga
Bayanan hoto, A Afrika Ta Kudu kuwa, ana amfani da jirgin ƙasa ne wajen jigilar riga-kafin korona zuwa garuruwan da ababen hawa ke wahalar shiga
Yadda wani mai goyon bayan sabon zaɓaɓɓen Shugaban Zambia Hakainde Hichilema ke kallon yadda ake bikin rantsuwar shugaban a Lusaka.
Bayanan hoto, Yadda wani mai goyon bayan sabon zaɓaɓɓen Shugaban Zambia Hakainde Hichilema ke kallon yadda ake bikin rantsuwar shugaban a Lusaka.
Yadda ƴan wasa masu laruran naƙasa daga Agola suka yi zaune a bayan fage yayin da ake gudanar da wasan a Tokyo a ranar Talata.
Bayanan hoto, Yadda ƴan wasa masu laruran naƙasa daga Angola suka yi zaune a bayan fage yayin da ake gudanar da wasan a Tokyo a ranar Talata.
Cikin waɗanda suke wasan na masu fama da naƙasa har da Ibrahim Elhusseiny daga Masar wanda zakara ne a ɓangaren wasan table tennis a ƙasarsa
Bayanan hoto, Cikin waɗanda suke wasan na masu fama da naƙasa har da Ibrahim Elhusseiny daga Masar wanda zakara ne a ɓangaren wasan table tennis a ƙasarsa.

Duka waɗannan hotunan suna da haƙƙin mallaka