Waiwaye: Muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya daga 29 ga Satumba zuwa 2 ga Oktoba

Independence Day
An wallafa

Mun kawo ƙarshen wannan makon mai cike da tarihi, inda Najeriya ta cika shekara 61 da samun ƴancin kai daga turawan mulkin mallaka. Bari mu yi duba kan muhimman abubuwan da suka faru a ƙasar daga 26 ga watan Satumba zuwa 2 ga watan Oktoba 2021.

Najeriya ta yi bikin cika shekara 61 da samun ƴanci

Ranar Juma'a 1 ga watan Oktoba ne Najeriya ta cika shekara 61 da samun ƴanci daga turawan mulkin mallaka na Burtaniya.

An yi shagulgulan murna sannan shugaban ƙasa ya gabatar da jawabi mai tsawo wanda ya taɓo abubuwa da dama da suka haɗa da tattalin arziƙi da tsaro da cutar korona da shafukan sada zumunta.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce wa ƴan Najeriya "Kyakkyawan fata da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya da nasarar Najeriya da ƴan ƙasar ke nunawa ce suka sa take ci gaba da kasancewa dunƙulalliya," a dandalin Eagle Square inda aka yi shagulgulan bikin.

Shugaban ya ayyana cewa "wata 18 ɗin da suka gabata sun kasance daga cikin mafiya wahala a tarihin Najeriya. Tun bayan yaƙin basasa, ina tababar idan mun ga wani lokaci da aka samu ƙaruwar ƙalubale kamar irin wanda muke gani a yanzu."

Nigeria at 61

Kalaman Bafarawa kan yankin arewa maso yammacin Najeriya

Tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma sanannen ɗan siyasa a arewa maso yammacin Najeriya Attahiru Bafarawa ya koka kan halin da yankin arewa maso yammacin Najeriya ke ciki dangane da batun tsaro.

Ya ce yana takaicin yadda mutanen yankin suka noma gonakinsu amma ba za su iya zuwa su girbe amfani ba saboda barazanar tsaro.

Alhaji Attahiru Bafarawa, ya ce ya kamata Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya zagaya sassan jiharsa don tantance tasirin matakan da ya ɗauka na kassara 'yan fashin daji da kuma ɓullo da matakan rage raɗaɗi ga jama'a.

Tsohon gwamnan ya kuma buƙaci Shugaba Muhammadu Buhari, da shi ma ya kai irin wannan ziyara ko ya tura wakilai don su je su tantance haƙiƙanin abin da ke faruwa yanzu a jihohin arewa maso yamma da ke fama da hare-haren 'yan fashin daji.

Hutun mako biyu ga angwayen ƙarni

Angon Ƙarni

Ranar Laraba 29 ga watan Satumba ne gwamnatin Najeriya ta ce ta amince da hutun mako biyu ga ma'aikata maza da matansu suka haihu, wato angwayen ƙarni, abin da ke nufin wani babban sauyi a tsarin dokokin aiki na kasar.

Matakin ya zo ne bayan da aka shafe shekaru biyu ana muhawara kan batun.

Shugabar Ofishin Ma'aikatan gwamnatin Najeriya Folasade Yemi-Esan ta ce an amince da matakin ne bayan taron majalisar koli a ranar Laraba, "don iyaye maza su samu sukunin kasancewa da jariransu a farko-farkon haihuwa."

Matakin gabatar da hutun haihuwa ga angwayen ƙarni na zuwa ne a lokacin da masu fafutuka suke ci gaba da neman cewa ya kamata maza ma a dinga ba su hutun haihuwa don su samu lokacin kula da matansu da jariransu - a wani ƙoƙari na sauya al'adar da ake barin mata kawai da dawainiyar haihuwa.

Hari a sansanin jami'an tsaro

Sojojin Najeriya

Wasu ƴan bindiga sun kai hari wani sansanin jami'an tsaro na haɗin guiwa a ƙaramar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto inda suka kashe jami'an tsaro a ƙalla 17.

A cikin jami'an tsaron da suka rasu akwai sojoji tara da jami'an tsaron farar hula na civil defense guda uku da ƴan sandan Mopol biyar.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun ƙona motocin sintiri biyu sannan suka yi awon gaba da wata motar.

Dama can al'ummar yankin sun koka kan abin da suka kira mamayar ƴan bindiga a yankin nasu.

Aminu Boza mai wakiltar sabon birni ta arewa a majalisar jihar Sokoto ne ya tabbatar wa BBC aukuwar lamarin kuma sun ce yankin nasu ya koma hannun yan bindiga domin babu jami'an tsaro.

Ɗan majalisar dokokin mai wakiltar Sabon Birni ta Kudu Honorabul Sai'du Ibrahim ya ce ''ɓarayin da a ka koro daga jihohin Zamfara da Katsina sun dawo Isa da Sabon Birni, kuma Sama da gari 500 a yankin sun watse sun yi Nijar.''

Zulum ya ce an sa siyasa a batun tsaro

Babagana Umara Zulum

Gwamnan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya Babagana Umara Zulum ya yi zargin cewa siyasa da aka sanya wajen ɗaukar jami'an tsaro a kasar ita ke ƙara dagula al'amura, abin da ya jefa harkokin tsaron ƙasar a hannun masu neman aiki.

Zulum ya bayyana haka a ranar Laraba lokacin da yake gabatar da wata maƙala a jihar Plateau.

Ya ce "babbar matsalar yadda ake ɗaukar aiki ne. Mafi yawan waɗanda ake ɗauka aiki a rundunar sojin Najeriya da ta ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro masu neman aiki ne kawai. Da yawa suna aikin ne domin basu da abin yi.

"Waɗanda aka ɗauka shekara 20 baya sun yi abin da ya kamata saboda suna da sha'awar aikin, amma na yanzu neman aikin kawai suke yi, babu sadaukarwa babu nuna damuwa," a cewar Zulum.

Zulum ya kara da cewa matukar ba muyi abin da ya dace ba, babu abin da zai tafi dai-dai.

Ƙarin labarai da za ku karanta: