Man City na farautar dan wasan tsakiyar Barca, Atletico na son Werner

..
Bayanan hoto, Serge Aurier
An wallafa

Ɗan wasan bayan Ivory Coast Serge Aurier mai shekara 28 wanda yanzu haka kwantiraginsa ta ƙare da Tottenham Hotspur, ya shirya komawa ƙungiyar nan ta Sifaniya Villarreal. (L'Equipe - in French)

Claudio Ranieri ya amince ya zama sabon kocin Watford bayan Xisco Munoz ya bar ƙungiyar a ranar Lahadi, inda ake sa ran kocin mai shekara 69 saka hannu a kwantiragi a ranar Lahadi. (Sky Sports)

Manchester City na bibiyar ɗan wasan tsakiyar Barcelona mai shekara 19 ɗan Sifaniya Nico Gonzalez. (Fichajes - in Spanish)

Ɗan wasan bayan Borussia Monchengladbach Luca Netz ya ce ya yi watsi da buƙatar ya koma Manchester City shekara uku da suka gabata, kuma ɗan wasan mai shekara 18 ya jaddada cewa zai sake watsi da buƙatar su. (Sun)

Tsohon ɗan wasan gaban Arsenal da Manchester United Alexis Sanchez bai san makomarsa ba a Inter Milan bayan ɗan wasan mai shekara 32 ɗan ƙasar Chile ya yi rubutu a shafin sada zumunta inda daga baya ya goge rubutun inda ya yi ƙorafi kan ƙarancin taka ledar da yake yi. (Mirror)

...
Bayanan hoto, Ɗan wasan gaban Chelsea Timo Werner

Atletico Madrid ta zama ƙungiya ta baya-bayan nan da ta shiga rububin neman ɗan wasan gaban Jamus Timo Werner mai shekara 25 daga Chelsea. (Transfer Market Web)

Tsohon ɗan wasan gaban Manchester City Yaya Toure mai shekara 38 ya tallata kansa ga Barcelona a daidai lokacin da ƙungiyar ke fuskantar ƙalubale, sai dai babu wani tabbaci ko ɗan wasan yana so ya taka leda ne ko kuma ya zama koci. (Sun)

Mike Ashley ya san cewa hanya daya kawai da za a bi a sauya wa Newcastle sabon koci ita ce a biya kusan duka kuɗin kwantiragin Steve Bruce wadda ya amince da ita tun a Yulin 2019. (Chronicle Live)

Ɗan wasan gaban Bayern Munich Joshua Zirkzee mai shekara 20 ya ce ya yi watsi da buƙatar Everton na ya sake sa hannu a kwantiraginsa a 2017. (Het Nieuwsblad via Liverpool Echo)