'Tsutsa ta yi wa masara illa a noman bana'

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar manoman masara a Najeriya ta sanar da cewa, 'ya'yan kungiyar sun fuskanci wasu 'yan matsaloli a daminar bana.
Rashin wadatar ruwan sama da ƙwari a daidai lokacin da masara ta soma kosawa na daga cikin matsalolin da manoman masara suka fuskanta a wasu yankunan arewacin Najeriya.
To sai dai tuni suka fara tunanin lalubo hanyoyin ƙara samar da yawan masara daga noman rani, duk da cewa wannan lamari ba zai hana samar da wadataciyar masara ga kasa baki daya ba.
Bello Annur Abubakar Funtuwa shi ne shugaban Kungiyar manoman masara ta kasa a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa "yanayin kakar bana sai godiyar Allah sakamakon an dade da fara girbi a wurare daban-daban a kasar musamman inda aka yi shukar wuri."
"Tun watan jiya suka fara girbin masara, ko kan hanya kana iya ganin yadda manoma suka baza masararsu domin ta bushe. Lamarin sai godiyar Allah duk da cewa a kowace shekara akan fuskanci kalubale ta wannan fanni."
Misali babban kalubalen da manoma masara suka fuskanta a bana shi ne tsutsar da ke kama zuciyar masara ta lalata ta.
Sai kuma a karshe-karshen an yi fama da matsalar daukewar ruwan sama a wasu yankunan Najeriya da hakan ya shafi noman masarar.
Annur ya kara da cewa rashin zubar ruwan sama zai shafi yawan masarar da manoman kasar ke samarwa a duk shekara.
"A bana mun yi kiyasin manoman Najeriya za su noma masara tan miliyan 20, amma saboda wannan rashin ruwa da matsalar tsutsa za a samu raguwa, amma muna fatan ba zai taka kara ya karya ba.
"Hakan zai samu ne saboda an kara bunkasa noman masara fiye da lokutan baya. A bara kadai bayan na gama noma na samu masara tan miliyan 20, shi y asa muka so fadada noman ya kai tan miliyan 25."
A karshe ya ce matukar ana son cike wannan giɓin to a gaggauta fara noman rani da mayar da hankali kan hakan.
Feshin maganin ƙwari da malaman gona suka aminta da shi na daya daga cikin hanyoyin rage asarar amfanin gona musamman ma dai ita masara da cikin ƙanƙanin lokaci tsutsa ke yi mata mummunar illa.



























